Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ajaero Ya Amsa Gayyatar ‘Yan sanda, Ya Dawo Lafiya - NLC


Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero, (tsakiya,) sanye da bakar riga, bayan da ya dawo daga amsa gayyatar 'yan sanda (Hoto: Facebook/NLC)
Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero, (tsakiya,) sanye da bakar riga, bayan da ya dawo daga amsa gayyatar 'yan sanda (Hoto: Facebook/NLC)

Kungiyar ta NLC ta sha alwashin tsunduma yajin aikin da zai tsayar da al’amuran kasar cik idan har aka tsare Ajaero.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta NLC a Najeriya, Joe Ajaero ya amsa gayyatar da ‘yan sanda suka aika masa a ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar.

A makon da ya gabata jami’an ‘yan sandan Abuja suka aika wa Ajaero wasikar gayyata kan zarginsa da sa hannu a ayyukan ta’adanci da laifukan yanar gizo, zargin da Ajaero da NLC suka musanta.

Da misalin karfe 10 na safe Ajaero, wanda ya samu rakiyar fitaccen lauya, Femi Falana da dan fafutukar kare hakkin bil Adama Deju Adeyanju, ya bar hedkwatar kungiyar ta NLC don amsa gayyatar.

Mambobin kungiyar ta NLC sun yi dandazo a hedkwatarsu inda suka yi ta rera wakokin nuna goyon baya ga shugabansu.

Kungiyar ta NLC ta sha alwashin tsunduma yajin aikin da zai tsayar da al’amuran kasar cik idan har aka tsare Ajaero.

Sai dai daga baya kungiyar ta NLC ta tabbatar da dawowarsa bayan da ya amsa gayyatar ‘yan sandan a ofishinsu na Abbatoir da ke mahadar Guzape a Abuja.

“Shugabanmu ya amsa gayyatar, ya kuma dawo. Mun kuma fada musu ba mu da wani abu da muke boye wa.” In ji Sakatare-Janar na kungiyar ta NLC, Emmanuel Ugboaja yayin da yake jawabi ga mambobin kungiyar.

Tun da misalin karfe 8 na safe shugabannin kungiyar ta NLC suka fara taruwa a ofishin na NLC.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG