Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Samamen Da Jami’an Tsaro Suka Kai Ofishin NLC


Zanga-zangar NLC
Zanga-zangar NLC

“Ga dukkan alamu, wannan samame da aka kai da daddare mai ban tsoro, wani yunkuri ne na razana 'ya'yan kungiyar." Amnesty ta ce.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta yi tir da samamen da jami’an tsaro suka kai hedkwatar kungiyar kwadago ta NLC da ke Abuja a Najeriya.

Rahotanni sun ce a daren ranar Laraba jami’an tsaron suka kai samamen inda suka yi kaca-kaca da ofishin suka kuma yi awon gaba da takardu da wasu kayayyaki da dama.

“Ga dukkan alamu wannan samame da aka kai da daddare mai ban tsoro, wani yunkuri ne na razana 'ya'yan kungiyar.

“A lokacin samamen, jami’an tsaron sun kwashi litattafai da sauran kayayyaki inda suka yi zargin cewa an yi amfani da su wajen tunzura jama’a don su yi zanga-zanga a kwanan nan.” In ji sanarwar da Amnesty ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Alhamis.

“Muna cikin damuwa game da yadda tsaron lafiyar jami’an kungiyar ta NLC zai kasance.” Sanarwar ta kara da cewa.

A gefe guda, gidan talabajin na Channels ya ruwaito hukumar tsaron farin kaya ta DSS tana nesanta kanta da samamen.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG