Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Muhammad Malagi da takwararsa karamar Ministar Kwadago da Ayyukan Yi, Nkeruka Onyejeocha suka bayyana hakan bayan kammala wata ganawar sirri tsakanin Shugaban Kasa Bola Tinubu da shugabannin hadaddiyar kungiyar kwadago a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja a yau Alhamis.
Wadanda suka halarci ganawar ta tsawon kusan sa’a guda sun hada da; shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero, da takwaransa na TUC, Festus Osifo da sauran ‘yan tawagarsu.
A cewar shugaban kungiyar TUC, tawagar ‘yan kwadagon ta shaidawa shugaban kasar irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fama dasu a yau.
“A yayin ganawar, mun yi kokarin mu baje komai a fili, al’amuran dake addaba tare da ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya a yau, da wahalhalun tattalin arziki, da faduwar darajar Naira da kuma yadda hakan ke shafar farashin kayayyakin masarufi a kasuwa.”
Shugaban kungiyar kwadago ta NLC yace ganawar ba ccinikayya bace kuma har yanzu dukkanin tayin da bangarorin 2 suka yi suna nan basu sauya ba.
A cewar Ajaero, “a zahiri, tattaunawar ba cinikayya bace mun sha yin irin haka a baya. Mun amince mu nazarci wasu muhimman batutuwa kuma me yiyuwa mu sake haduwa a mako mai zuwa. Wannan ita ce matsayar da muka cimma saboda bamu je don tattauna batun kudi ba.
“Akalla dai akwai wasu muhimman batutuwa da muka cimma matsaya akansu. Kowa zai cigaba da zama akan bakansa dangane da tayin Naira dubu 250 da dubu 62 da aka gabatar har sai an kammala tattaunawar.”
Dandalin Mu Tattauna