Gobara ta tashi a kasuwar tufafi ta Kano da aka fi sani da Kantin Kwari da tsakar daren Lahadi, inda ta lakuma shaguna 10 a daya cikin rukunin shagunan dake kasuwar.
Gobarar wacce ta tashi a wani ginin dake kan titin Gidan Inuwa Mai Bayajidda dake da fiye da shaguna 100, ta lakume ilahirin tufafin dake cikin shaguna 10 inda ta haddasa barnar miliyoyin nerori.
Shaidun da suka shaida afkuwar lamarin sun ce sun yi iya bakin kokarinsu na shawo kan wutar tare da ceto wani bangare na dukiyar gabanin zuwan jami’an kashe gobara.
Hukumar kashe gobara ta Kano ta bayyana musabbabin tashin gobarar da matsalar lantarkin solar.
Hukumar gudanarwar kasuwa tufafi ta Kantin Kwari ta bukaci inganta matakan kiyaye afkuwar hatsari domin kaucewa sake tashin gobarar a nan gaba.