Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya 500 Ne Suka Yi Rajista Don A Kwaso Su Daga Lebanon – Ma’aikatar Harkokin Waje

Wata tawagar 'yan Najeriya da aka kwaso daga Sudan bayan barkewar rikici a kasar a bara (Hoto: Twitter/NIDCOM) - A kiyaye: Mun yi amfani da wannan hoto ne a matsayin misali.
Wata tawagar 'yan Najeriya da aka kwaso daga Sudan bayan barkewar rikici a kasar a bara (Hoto: Twitter/NIDCOM) - A kiyaye: Mun yi amfani da wannan hoto ne a matsayin misali.

Sanarwar ta yi kira ga dukkan 'yan kasa mazauna Lebanon da kada su ki yarda a kwashe su domin rikicin da ke faruwa na iya tsananta.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce ya ‘yan Najeriya mazauna Lebanon 500 ne kadai suka yi rajista don a kwashe su daga kasar yayin da rikicin Isra’ila da Hezbollah ke kara kta’azzara.

“Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a halin yanzu kimanin 'yan Najeriya 500 ne suka yi rijista da Ofishin Jakadancin Najeriya, sai dai ta kara da cewa sama da 'yan Najeriya 2000 ne ke zaune a kasar.” Wata sanarwar dauke da sa hannun Kakakin ma’aikatar Eche Abu-Obe ta ce.

Ma’aikatar harkokin wajen ta Najeriya ta ce kara da cewa “Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara shirin kwashe 'yan Najeriya mazauna Lebanon, sakamakon rikicin da ke kara ta'azzara tsakanin Isra'ila da Hezbollah.”

A cewar sanarwar, yanayin tsaro da ke kara tabarbarewa a Lebanon ya sa Gwamnati ta kaddamar da matakan gaggawa domin tabbatar da kwashe 'yan kasa cikin gaggawa don mayar da su zuwa gida nan ba da jimawa ba.

Sanarwar ta yi kira ga dukkan 'yan kasa mazauna Lebanon da kada su ki yarda a kwashe su domin rikicin da ke faruwa na iya tsananta.

Har ila yau sanarwar ta yi kira ga 'yan kasa da su bi ka'idojin tsaro, ta kuma yaba da kyakkyawar fahimtar da kasashen duniya ke nunawa, sannan ta yi alkawarin ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG