Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cinna Wa Sakatariyoyin Kananan Hukumomin Ikwere Da Eleme Wuta


Sabuwar sakatariyar karamar hukumar Ikwerre
Sabuwar sakatariyar karamar hukumar Ikwerre

Hakan dai ya biyo bayan janye jami’an ‘yan sandan dake tsaron sakatariyoyin kananan hukumomi 23 da kwamishinan ‘yan sanda jihar ya yi.

An cinnawa sabuwar sakatariyar karamar hukumar Ikwerre dake yankin Isiokpo wuta.

Wani mazaunin yankin ya tabbatarwa tashar talabijin ta Channels da afkuwar hakan a yau Litinin sannan faya-fayan bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta sun nuna ginin gudanarwar sakatariyar yana ci da wuta.

Hukumomin ‘yan sanda basu ce komai ba a kan lamarin kuma har yanzu ba a kai ga tantance yawan asarar da aka yi ba.

Hakan dai ya biyo bayan janye jami’an ‘yan sandan dake tsaron sakatariyoyin kananan hukumomi 23 da kwamishinan ‘yan sanda jihar ya yi.

Tunda fari, an cinnawa wani sashe na ginin sakatariyar karamar hukumar Eleme wuta.

Wani tsohon jakada, Oji Ngofa, wanda ya fito daga garin Eleme ya shaidawa tashar talabijin ta Channels cewa sabon zababben shugaban karamar hukumar Brian Gokpo ya ziyarci sakatariyar a bisa rakiyar kansiloli da magoya bayansa.

A cewarsa, shugaban karamar hukumar, ya kuma gano wasu daga cikin gine-ginen karamar hukumar suna ci da wuta.

Sabon shugaban karamar hukumar da kansiloli da magoya bayansa sun sha alwashin karbe iko da sakatariyar ta kowane irin hali.

A karamar hukumar Emohua ma, wasu mutane da ba’a san ko su wane ne ba datse kofar shiga sakatariyar.

Mutanen na nuna turjiya ne da kama aikin sabon shugaban karamar hukumar, David Omereju. a cikin wani bidiyon daya karade kafafen sada zumunta an jiyo suna cewa “babu jihar Ribas in ba Wike!!”

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG