Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Da 'Yayansa A Jihar Kebbi


Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasir Idris
Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasir Idris

Matsalar rashin tsaro na cigaba da daukar sabon salo, inda yanzu 'yan bindiga ke kai hare-hare tare ta yin garkuwa da sarakuna da iyalan su kamar dai yadda ya faru ga sarkin Kanya da na Rafin Gora a jihar Kebbin Najeriya.

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da daukar sabon salo, inda 'yan bindiga ke kai hare-hare tare ta yin garkuwa da sarakuna da iyalansu.

Irin haka ne ya faru a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya inda 'yan bindiga suka sace Sarkin Kanya suka kuma yi garkuwa da 'yayansa biyu, da kuma 'ya'yan Sarkin Rafin Gora da wasu mutane na yankin.

Duk da kokarin da jami'an tsaro ke yi har yanzu a iya cewa da sauran rina a kaba, domin har yanzu 'yan bindiga na da kuzarin kai hare-hare tare da kisan mutane.

Gwamnatin jihar ta Kebbi ta bakin Mataimaki na musamman ga gwamnan akan sadarwa, Abdullahi Zuru ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma ta ce bayan daukar sarkin an kuma dauki 'ya'yansa biyu da kuma 'ya'yan Sarkin Rafin Gora su biyu mata, kuma kawo yanzu ba a ji komai ba daga barayin.

Sai dai har yanzu mutane na tambaya kan irin matakan da aka dauka don kaucewa irin abin da ya faru a Sakkwato, inda 'yan bindiga suka sace Basarake har ya yi fiye da mako uku a hannunsu, inda a karshe suka kashe shi.

Masu lura da lamurran yau da kullun na ganin cewa wannan lamari da ke faruwa a yanzu inda barayi suka karkata ga satar sarakuna abu ne na tashin hankali.

Farfesa Tukur Muhammad Baba Dan Iyan Mutum biyu ya ce dole ne mahukunta su kara tashi tsaye wajen dakile wannan bala’i na ayyukan 'yan bindiga baki daya.

Idan dai ba a manta ba 'yan bindiga sun sace babban basaraken Gobir na jihar Sakkwato a ranar Asabar 27 ga watan Yuli na shekarar 2024, suka kashe shi a ranar 20 ga watan Agusta, abin da har yanzu wasu jama'a ke ci gaba da juyayi akai.

Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi tuni dai ta tabbatar da aukuwar wannan abin alhini.

A saurari cikakken rahoton a sauti tare da Muhammad Nasir.

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Da Yayansa A Jihar Kebbi
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG