Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Ribas: An Bude Sakatariyoyin Kananan Hukumomi Bayan Rantsar Da Shugabanninsu

Gwamnan jihar Rivers a Najeriya, Siminalayi Fubara (Facebook/Fubara)
Gwamnan jihar Rivers a Najeriya, Siminalayi Fubara (Facebook/Fubara)

A watan Yunin da ya gabata aka rufe sakatariyoyin sakamakon takaddamar da ta kunno kai tsakanin kantomomin rikon dake biyayya ga gwamna Siminalayi Fubara da tsaffin shugabannin kananan hukumomin, wadanda ke biyayya ga Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, Abuja.

Rundunar ‘yan sandan ribas ta bada umarnin sake bude ilahirin sakatariyoyin kananan hukumomin jihar 23 biyo bayan gudanar da zabe da rantsar da sabbin shugabanninsu da aka yi.

Sanarwar da kakakin rundunar, Grace Iringe-Koko, ta fitar da safiyar yau Litinin ce ta tabbatar da hakan.

A cewarta, sabon kwamishinan ‘yan sandan da aka tura jihar, Mustapha Bala a bisa biyayya ga umarnin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ba da umarnin janye jami’an ‘yan sandan da aka tura su tsare sakatariyoyin kananan hukumomin dake fadin jihar nan take.

A watan Yunin da ya gabata aka rufe sakatariyoyin sakamakon takaddamar da ta kunno kai tsakanin kantomomin rikon dake biyayya ga gwamna Siminalayi Fubara da tsaffin shugabannin kananan hukumomin, wadanda ke biyayya ga Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, Abuja.

Janye jami’an ‘yan sandan daga sakatariyoyin kananan hukumomin na zuwa bayan da gwamna Siminalayi Fubara ya rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomin da aka zaba a jihar.

Rantsarwar da ta gudana a dakin taro na fadar gwamnatin jihar dake Fatakwal, babban birnin jihar a jiya Lahadi, na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar zaben jihar Ribas (RSIEC) ta gudanar da zaben kananan hukumomi.

Tunda fari a jiya Lahadi, RSIEC ta mika takardun shaidar cin zabe ga sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomin.

Bayan kammala zaben da ya gudana cikin tsananin fargaba, jam’iyyar APP ta lashe kujerun ciyamomi 22 daga cikin 23, a yayin da jam’iyyar AA da lashe kujera 1.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG