Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC), Olanipekun Olukoyede ya bayyana cewar, efcc ta gaza gudanar da bincike a jihohin Najeriya 10 ne, saboda dimbin umarnin kotun dake hanata yin hakan.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a yayin karo na 6 na taron bada horon hadin gwiwa tsakanin EFCC da cibiyar horas da harkokin shari’a ta Najeriya (NJI) da aka shirya domin alkalai a babban dakin taron cibiyar dake birnin Abuja.
EFCC ta bayyana cewar taken taron na “shigar da masu ruwa da tsaki cikin yakin da akeyi da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa,” ya dace.
Duk da cewa Olukoyede bai bayyana jihohin da al’amarin ya shafa ba, saidai, ya koka da yadda umarnin kotu ke cigaba da yiwa ayyukan hukumar efcc na binciko badakala tarnaki.
A cewarsa, daga cikin dimbin matsalolin dake yiwa EFCC tarnaki harda yawan dage manyan shari’o’in cin hanci da rashawa da zargin yiwa kotu raini da kuma yawan dogewa akan dabarun shari’a.
Ya kara da cewar, wajibi ne a kawo karshen yanayin da mutumin da ake tuhuma zai garzaya kotu ya samo umarnin kotun da zai hana EFCC kama shi.
Dandalin Mu Tattauna