Ya Kamata Gwamnati Ta Kawo Karshen Yajin Aikin Malaman Jami’o’i - Masu Zanga-Zanga

Kungiyar NLC Na Zanga Zanga A Harabar Majalisar dokokin Najeriya

A ci gaba da zangar zangar nuna goyon baya ga kungiyar malaman Jami'o'in Najeriya, ASUU, wadda ke nemar ingantaccen yanayin aiki, masu zanga zangar na kiran gwamnati ta gaggauta sauraron ASUU.

A yayin da zanga-zangar lumanar da kungiyar kwadago ta Najeriya ta kira don neman gwamnati ta dauki matakin kawo karshen yajin aikin malaman jami’o’in kasar ta shiga kwana na 2, masu ruwa da tsaki da suka hada da kungiyoyin malaman jami’o’i, gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya, da sauran masu ruwa da tsaki sun jaddada mahimmancin gwamnati ta biya bukatun malaman ko ba don komai ba, don a kawar da matsaloli kamar shiga shaye-shaye ko lalacewar tarbiyyar daliban.

Kungiyar NLC Na Zanga Zanga A Harabar Majalisar dokokin Najeriya

Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewa, Alh. Nastura Ashir Sahriff, da ke zama daya daga cikin jiga jigai da suka shiga gaba a wannan zanga-zangar lumanar dai ya ce idan aka saurari koke-koken malaman, akwai alamun gwamnati ba ta da gaskiya cikin wannan al'amari la’akari da yadda gwamnati ta bukaci malaman su kawo tsarin biyansu albashi kuma suka mika mata, aka tantance ingancin tsarin kuma gwamnati ta ki sa hannu a kan tsarin, an yi kuskure.

Kungiyar NLC Na Zanga Zanga A Harabar Majalisar dokokin Najeriya

A cewar Nastura, ya kamata gwamnati ta mutunta ilimi ta kuma mayar da shi abu mai mahimmanci ya na mai cewa zalinci ne a ce an wayi gari sai 'yan Najeriya sun nemi ilimi ta hanyar zuwa makarantun kudi kawai.

Daya daga cikin jiga-jigan kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC wanda ke da yara biyu a jami’o’in kasar, Mal. Ibrahim Yusuf, ya bayyana cewa abun takaici ne ‘yan Najeriya su tsinci kansu cikin yanayin da suka sami kansu musamman na tabarbarewar ilimi a kasar inda yara suka shafe sama da watanni 5 a gida ba sa zuwa makaranta.

Kungiyar NLC Na Zanga Zanga A Harabar Majalisar Dokokin Najeriya

Shi ma Kwamared Yunus Yusuf, mamba a kungiyar manyan malaman jami’o’i wato SSANU reshen jami’ar Abuja, ya ce sun fito ne don nuna goyon baya ga kungiyar NLC a fafutukar da take don ganin daliban jami’o’in gwamnatin Najeriya sun koma bakin karatunsu nan take ba tare da ci gaba da bata lokaci ba.

A cewar Kwamared Yunus Yusuf, kungiyoyin basu ga alamar gwamnati ta shirya warware wannan al'aamari nasu ba la’akari da yadda ta ware kungiyar ASUU kawai cikin kungiyoyin jami’o’in 4 kamar su SSANU, NASU da ma NAAT ta dauki mataki ba tare da shigar da dukkansu ciki ba, inda ya yi kira ga gwamnati ta dubi yanayin da daliban ke ciki ta dauki matakin da ya dace cikin gaggawa.

Kungiyar NLC Na Zanga Zanga A Harabar Majalisar Dokokin Najeriya

A baya-bayan nan ne kungiyar NLC dai ta kira dukkan yan Najeriya da su shiga wannan zanga-zangar lumana don farkar da gwamnati daga baccin da take ciki tare da yin gargadin cewa idan gwamnati bata dauki matakan da suka kamata ba cikin gaggawa, zata dauki matakin gaba na ma’aikatan kasar su shiga yajin aikin gamagari.

A kwanakin baya-bayan nan ne mataimakin shugaban kungiyar malaman jami'o'i wato ASUU, Kwamared Christopher Piwuna, ya ce muddin gwamnati bata biya musu bukatunsu ba, ba za su janye yajin aikin da suka shafe tsawon sama da watanni 5 suna yi ba, inda ya yi kira ga dalibai su shiga cikin zanga-zangar da NLC ta kira don gwamnati ta ji kokensu.

Idan ana iya tunawa, tun cikin watan Febrairun shekarar 2022 da mu ke ciki ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin gargadi da ya rikide zuwa wannan lokaci domin neman gwamnatin kasar ta biya mata bukatunta, kafin daga bisani kungiyoyin manyan malaman jami’o’i ta SSANU, NAAT da NASU suka shiga su ma.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:

Your browser doesn’t support HTML5

Kiran Masu Zanga Zanga Ga Gwamnati.mp3