Wannan na zuwa ne biyo bayan labarin mika rahoton kwamitin shiga tsakani da gwamnati ta kafa a watan Maris na shekarar nan ya kai ga kunnuwan bangaren manyan malaman jami’o’i suna mai cewa babu hannun su a cikin rahoton kwamitin, sai an koma kan teburin tattauna la’akari da cewa ASUU da kwamitin suka tsaida matsaya ba tare da tafiya da su ba.
Yajin aikin da ake fama da shi a bangaren jami’o’in Najeriya dai ya dauki sabon salo ne a yayin da mambobin kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i ta SSANU da kungiyar ma’aikatan jami’o’i ta NASU suka yi watsi da rahoton kwamitin da aka koma kan teburin tattaunawa da shi tsakanin gwamnatin Tarayya da kungiyoyin wanda Farfesa Nimi Briggs ke jagoranta na neman ya gagari kundila a yanzu.
Shugaban kungiyar manyan malaman jami’o’i ta SSANU, Mal. Muhammad Haruna, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, ba za su yi aiki da shawarwarin kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin kawo karshen yajin aikin da ake ciki ba a yanzu saboda sau biyu kawai aka tattauna da su kuma kwatsam suka ji labarin an mika rahoton kwamitin ga gwamnati.
Mataimakin shugaban kungiyar malaman jami’o’in Najeriya wato ASUU, Christopher Piwuna, ya yi cikakken bayani a game da wannan al’amarin nasu tare da bayyana cewa zasu shiga zanga-zangar lumana da kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, ta kira a fadin kasar don nunawa gwamnatin sun gaji da barin ‘ya’yansu dalibai a gida.
Da yake tsokaci a game da kira da kungiyar ASUU ta yi na cewa dalibai su shiga cikin zanga-zangar lumanar da NLC zata jagoranta a cikin mako mai zuwa, wani dalibi ya ce.
Idan ana iya tunawa dai, a cikin watan Maris ne gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Farfesa Nimi Briggs domin tattaunawa da kungiyoyin jami’o’in kasar da suka hada da NASU, SSANU, NAAT da kuma kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU a matsayin wani yunkuri na warware rikicin da ke faruwa a bangaren jami’o’in kasar.
Kungiyar ASUU dai ta dakatar da harkokin ilimi a jami’o’in gwamnati tun ranar 14 ga watan Fabrairu lokacin da malaman suka fara yajin aikin, lamarin da ya kara rincabewa bayan da kungiyoyin NASU da SSANU su ma suka dakatar da aikinsu don neman gwamnati ta biya musu bukatu a watan Afrilun shekarar 2022.
Duk kokarin ji ta bangaren gwamnati kan wannan al’amari tsakanin kwamitin da ta kafa da kungiyoyin malaman jami’o’in kasar hudu dai ya ci tura.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: