Kakakin Majalisan Dokokin Ghana Ya Soki Shugaban Kasar Bisa Jinkiri Wajen Sanya Hannu A Kudirin Dokar Haramcin Auren Jinsi

Majalisar kasar Ghana

Kakakin Majalisar dokokin Ghana ya ce kin amincewa da sanya hannu a kudirin haramcin auren jinsi ta LGBTQ da shugaba Nana Akufo-Addo yayi ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, kuma Majalisar za ta daina amincewa da sabbin nade-naden Ministoci.

Jawabin kakakin majalisan na zuwa ne biyo bayan shugaban kasar Nana Addo ya nuna cewa ba zai sanya hannu akudirin dokar haramcin auren jinsi ba har sai kotun kolin kasar ta zantarda hukunci akan wasu bukatu da aka gabatar gunta mai nasaba da kudirin dokar haramcin auren jinsi a kasar.

Kakakin Majalisar Alban Bagbin ya shaidawa ‘yan majalisar a ranar Laraba cewa, "Majalisar dai ba ta iya ci gaba da amincewa da nade naden mai girma shugaban kasa ba har sai bayan kotun koli ta bayyana sakamakon bukatu da aka gabatar mata"

Matakin Shugaban Majalisan ya haifar da cece-kuce tsakanin wakilan Majalisan inda masu rinjayin suka soki matakin da Shugaban Majalisar ya dauka na dakatar da amincewar ministoci da yawansu ya kai 21 ciki har da kananan Ministocin kudin kasar tare da bayyana hakan a matsayin rashin bin tafarkin dimokradiyya tare da hana Shugaban kasa da Ghana samun ƙwararrun maza da mata da za su taimaka wajen tafiyar da ayyukan gwamnati.

FILE PHOTO: Ghana LGBTQ+ activists see church blessings as distant luxury

"A matsayinmu na masu rinjayi bamu amince da matsayin shugaban Majalisan dokokin ba" inji shugaban masu rinjayi a Majalisan Afenyo Markin.

Su kuwa marasa rinjayi na ganin wannan mataki shine mafi a'ala sabida gaza sanya hannu akan kudirin dokar haramcin auren jinsi ya saba wa dokan kasar.

Casiel Ato Forson shine shugabansu, ya kuma ce "Shugaba Akufo Addo ya dauki wani matsayi na ban mamaki wanda kundin tsarin mulkin kasar Ghana bai sani ba"

Tsamari tsakanin bangare majalisan dokokin kasar da ofishin shugaban kasa zai iya haifar da babban cikas ga demokradiyya tare da cigaban kasar har in ba'a samu daidaituwa tsakanin bangarori biyun ba inji Mallam Shariff Abdul salam masanin doka kana mai sharhi akan alumarran yau da kullum .

" an samu cikas makamancin wannan a lokacin tsohon Shugaban kasa dakta Hilla Liman a lokacin da gwamnatinsa ta gabatar da kasafin kudin kasa a Majalisan dokokin kasar inda aka samu rashin fahimta tsakanin wasu Ministoci har suka maka juna a kotu . Hakan ya janyo kifar da gwamnatinsa, don haka ya kamata mu dau darasi kan wannan al'amari da ya faru shekaru kusan 40 da suka gabata."

Kudirin dokar haramcin auren jinsi da majalisan ta amince da shi a watan da ya gabata har in shugaban kasa ya sanya hannu akai zai sanya hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin kazalika masu tallafa ma kungiyoyin zasu fuskanci hukuncin daurin shekaru biyar a gidan kaso.

Kungiyar Amnesty International ta yi gargadin cewa, kudirin "yana haifar da babbar barazana ga hakkoki da 'yancin" mutanen LGBTQ.

Amma kuwa Shugaban ya yanke shawarar dakatar da sanya hannu a kudirin ne bayan da ma'aikatar kudi ta yi gargadin cewa kudirin na iya janyo cikas a kokarin da gwamnatin kasar ke yi wajen samun tallafin dala miliyan 3.8 daga bankin duniya tare da dakile shirin lamuni na dala biliyan 3 daga IMF.

Saurari rahoton Hamza Adams:

Your browser doesn’t support HTML5

Cece-kuce Kan Kudirin Dokar Haramcin Auren Jinsi Da Majalisar Ghana Ta Zartar