A jawabinsa na farko a jiya Litinin kan amincewa da kudirin dokar, ya ce Ghana ba za ta ja da baya ba kan batun kare hakkin bil'adama, ya kuma kara da cewa an kalubalanci kudurin a kotun koli.
Akufo-Addo a cikin wata sanarwa ya ce "A yau ne na san cewa an shigar da kara a kotun koli." Ya kara da cewa "A halin da ake ciki, abin da ya dace shi ne mu jira hukuncin Kotu kafin a dauki wani mataki."
Kudirin na iya haifar da asarar dala biliyan 3.8 na tallafin bankin duniya a cikin shekaru biyar zuwa shida masu zuwa idan har ya zama doka, lamarin da zai kawo cikas ga shirin lamuni na dala biliyan 3 na IMF, in ji ma'aikatar kudi a cikin wata takarda da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani a ranar Litinin.
Kudirin zai bukaci sa hannu Akufo-Addo kafin ya zama doka.
A ranar 28 ga watan Fabrairu ne 'yan Majalisar suka amince da dokar da za ta kara kaimi wajen yaki da 'yan madigo, 'yan luwadi, da masu canza jinsi da wadanda ake zargi da tallatawa masu aikatawa.
Amincewa da kudirin na zuwa ne a daidai lokacin da Ghana ke kokarin fita daga cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki da tabarbarewar basussuka tare da taimakon shirin lamuni na asusun lamuni na duniya da aka samu a bara da kuma samun kudade daga bankin duniya.
Amurka ta ce ta damu matuka da kudurin dokar, ta kuma bukaci da a sake nazari a kan "ka'idar kundin tsarin."
A cikin daftarin cikin gida, ma'aikatar kudi ta ce asarar kudaden da bankin duniya ta yi zai yi mummunan tasiri ga ajiyar kudaden ketare da kuma daidaiton farashin musaya.
Ya kara da cewa, hakan zai iya "kashe" shirin na IMF, wanda zai haifar da mummunan yanayin kasuwa wanda zai shafi daidaiton farashin musaya, in ji shi.
Dandalin Mu Tattauna