Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Addini A Malawi Sun Yi Zanga-Zangar Nuna Rashin Amincewa Da Auren Jinsi Daya


Malaman Addini A Malawi yayin da su ke Zanga-Zangar Nuna Rashin Amincewa Da Auren Jinsi Daya
Malaman Addini A Malawi yayin da su ke Zanga-Zangar Nuna Rashin Amincewa Da Auren Jinsi Daya

Masu zanga-zangar sun fito ne daga manyan addinan kasar biyu - Kiristanci da Musulunci.

Shugabannin addinai a Malawi sun jagoranci zanga-zangar nuna adawa da auren jinsi a ranar Alhamis, tare da daruruwan mutane a Blantyre, babban birnin Malawi, domin nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira yunkurin halatta auren jinsi a kasar.

Masu zanga-zangar sun fito ne daga manyan addinan kasar biyu - Kiristanci da Musulunci.

Wasu yan luwadi
Wasu yan luwadi

Babban limamin coci, Thomas Luke Msusa ne ya jagoranci zanga-zangar a Blantyre. Ya ce auren jinsi zunubi ne, kuma halatta irin wannan auren zai kai ga musibar gushewar bil’adama.

Ya ce "idan muka canza yadda muke rayuwa a matsayin iyali, hakan na nufin za mu kare baki daya." "Idan muka ci gaba da aurar da namiji da namiji, tabbas za mu kasence babu zuri'a, babu 'ya'ya, ba rayuwa a duniya, ba rayuwa a Malawi."

Luwadi laifi ne a Malawi kuma hukuncinsa shi ne akalla daurin shekaru 14 a gidan yari.

Wasu yan luwadi
Wasu yan luwadi

Duk da haka, kungiyoyin fararen hula sun bayyana damuwarsu game da wariyar da 'yan madigo, luwadi, auren jinsi da sauran ‘yan kungiyar (LGBTQ) ke fuskanta a cikin kasar.

Michael Kaiyatsa, babban daraktan cibiyar kare hakkin bil’adama, ya ce malaman addini na da ‘yancin gudanar da zanga-zanga kan duk wani abu da suke ganin laifi ne, amma kuma ya kamata su yi la’akari da hakkokin sauran kungiyoyi.

Eric Sambisa, babban darektan kungiyar Nyasa Rainbow Coalition, mai fafutukar kwato 'yancin kungiyar ‘yan luwadi da madigo ta LGBTQ a Malawi, ya ce abin bakin ciki ne yadda shugabannin addinai ke goyon bayan wariya.

Coci wuri ne mai karfi a cikin al'umma," in ji shi. "Kuma ganin yadda cocin ke kan gaba wajen gudanar da zanga-zanga na iya haifar da tashin hankali a kan al'ummar da take cikin matsaloli. Don haka, abin bakin ciki ne yadda hakan ke faruwa."

Sambisa ya shaidawa Muryar Amurka cewa ya shiga buya ne biyo bayan barazanar kisa daga wasu da da ke kiransa suna boye sunansu. Barazanar ta zo ne 'yan makwanni bayan da aka kona ofishinsa a Blantyre.

A zanga-zangar ta ranar Alhamis, masu zanga-zangar sun gabatar da koke ga ofishin hakimin gundumar, inda suka bukaci ‘yan majalisar da kada su amince da duk wani kudiri ko zartar da wata doka da ke yunkurin halatta auren jinsi.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG