Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Za Ta Fara Hukunta 'Yan Luwadi Da Madigo


Wasu maza 'yan luwadi
Wasu maza 'yan luwadi

A yayin da batun ‘yan luwadi da ‘yan madigo da ta masu auren jinsi ke ci gaba da haddasa mahawara a kasashe daban-daban hukumomin Jamhuriyar Nijar sun jaddada aniyar kafa dokokin hukunta wadanda aka kama da aikata irin wadanan dabi’u a kasar.

Wannan na zuwa ne biyo bayan da kwamitin kula da gyaran fuskar kundin shara’a da kundin hukunta laifuka ya damka wa ministan shara’a rahotonsa mai kunshe da wasu sabbin kudurori ciki har da wadanda ake shirin gabatar da su a gaban majalisar dokokin kasa da zummar haramta luwadi da madigo da auren jinsi.

La’akari da cece-kucen da batun ‘yan luwadi da ‘yan madigo da masu auren jinsi ya haifar a tsakanin jama’ar Nijer bayan bayyanar wani bidiyon tsiraicin da wasu ‘yan mata suka yada a kafafen sada zumunta ya sa kwamitin da aka dora wa alhakin kwaskwarima ga kundin shara’a wato Code Penale bullo da wasu kudurorin doka don gabatar wa gwamnatin kasar.

Da yake Karin bayani akai shugaban kwamitin mai shara’a Maman Sani Ousseini Djibaje ya ce da zaran majalissar dokokin kasa ta yi na’am da wadanan shawarwari a nan gaba wadanda aka kama da aikata wannan dabi’a za su fuskanci hukunci.

Wasu masu luwadi da aka kama
Wasu masu luwadi da aka kama

Haka kuma wadanan dokoki sun yi tanadin taka burki ga kungiyoyin da ke kiran kansu na rajin kare hakkin ‘yan luwadi da masu madigo inji mai shara’a Djibaje.

Ainahi ‘yar majalisar dokokin kasa Nana Joubie Harouna Maty ce ta gabatar da bukata a majalisar dokoki don ganin an dauki matakan kare al’ummar Nijer daga wasu bakin al’adun da ke barazanar gurbata tarbiyar yara.

Koda yake akwai alamun tafiya ta kama hanya ‘yar majalissar na ganin har yanzu da sauran aiki.

Shigar matan da wasu bakin haure maza suka yi a lokacin da suka yada zango a birnin Agadez a makon jiya ya haifar da ta da jijiyoyin wuya a wajen al’umma da ke daukar lamarin tamkar wani abin da aka tsara takanas da nufin tsokana, to amma tsoma bakin dattawa ya kwantar hankula.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG