GOMBE, NIGERIA - Bayanai sun yi nuni da cewa, taron ya fake ne da bikin zagayowar shekara saboda jinsi maza da maza a lokacin sai asirinsu ya tonu.
Kamar yadda rahoto ya nuna, an kama matasan ne a lokacin suna gudanar da bukukuwan zagayowar shekarar haihuwa da kuma murnan kulla aure.
A tattaunawa da kwamandan rundunan jami’an tsaron farin kaya a jihar Gombe, Muhammed Mu'azu, ya ce sun samu nasarar kame matasan ne, sanadiyar rahoto na sirri da suka samu.
Ganin cewar ‘yan adam suna da 'yancin gudanar da abubuwan da suke so, muddin bai ci karo da dokar kasa ba, sai muka tuntubi, shugaban kungiyar kare hakkin ‘dan adam shiyyar Arewa Maso Gabas, Aliyu Muhammed Wayas, wanda ya shaida mana cewa auren jinsi a jihar Gombe walau na maza da maza ko kuma mata da mata laifi ne a jihar da ya saba doka.
Saurari cikakken rahoto daga Abdulwahab Muhammad:
Dandalin Mu Tattauna