Majalisar dokokin Ghana ta amince da kudurin dokar hana auren jinsi mai cike da cece-kuce bayan an shafe kusan shekaru uku ana tattaunawa.
Sabon kudirin dokar ya sanya hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari ga duk wanda aka samu da laifin.
Kazalika masu tallafawa kungiyoyin zasu sha daurin shaikaru biyar.
Tuni wasu kungiyoyin kare hakkin bil Adama guda 18 sukayi barazanar maka Shugaban Kasar a kotu har in ya amince ya sanya hannu akan kudirin saboda dokar zai tauye hakkokin marasa rinjayi a kasar, inji su.
A saurari cikakken rahoton Hamza Adams:
Dandalin Mu Tattauna