WASHINGTON, D. C. - A ranar 26 ga watan Yuli ne dai jami’an soji suka hambarar da zababben Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, kuma suka yi fatali da kiraye-kirayen da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar ECOWAS ta Afirka ta Yamma da sauran su suka yi na a maido da shi bakin aiki, lamarin da ya sa kasashen yankin suka ba da umurnin cewa dakarunsu su zauna cikin shiri.
A yayin ganawar tasu ta kwanaki biyu, wacce aka kammala da bikin rufewa daga misalin karfe 1600 agogon GMT, hafsoshin tsaron sun tattauna kan dabaru da sauran abubuwan da za a iya turawa, kamar yadda jadawalin hukuma ya nuna.
Har yanzu dai amfani da karfin soji ya kasance mataki na karshe, amma “idan komai ya gaza, jaruman kasashen yammacin Afirka, a shirye suke su amsa kiran aiki,” in ji kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS Abdel-Fatau Musah, a farkon taron a ranar Alhamis.
Ya ce akasarin kasashe 15 na kungiyar a shirye suke su shiga cikin rundunar tsaron ko-ta-kwana, in ban da wadanda suke karkashin mulkin soja, na Mali, Burkina Faso da Guinea da kuma karamar kasar Cape Verde.
-Reuters