Hadimin Biden a kan kwamitin karbar mulki, Jen Psaki shine ya bayyana kalaman kafin ganawar da Biden dan kansa ya halarta a karon farko tun bayan da ya lashe zaben tare da kakakin majalisa Nancy Pelosi da kuma shugaban Democrat a majalisar dattawa Chuck Schummer. Shugaban kasa na Democrat mai jiran gado, ya amshi bakwancin kusoshin Democrat a majalisun kasar ne a babban ofishinsa na wucin gadi dake Wilmington a jihar Delaware a jiya Juma’a.
Biden ya gana da Schummer da Pelosi da mataimakiyarsa Kamala Harris ne yayi da dukkansu ke saye da kyallen rufe huska kana suka nesanta da juna a kan teburi.
Pelosi ta fada a wani taron manema labarai kafin ganawar cewa, ita da Schummer, zasu tattauna da Biden game da murkushe cutar cikin gaggawa, da kuma yanda zasu yi amfani da majalisar dake kammala aiki su yi dokar da zata ci gaba da tallafin gwamnati da kuma taimakon COVID-19.
Amma har yanzu babu tabbas game da batun bada tallafin cutar a wannan shekara. Pelosi ta ce tattaunawa da suka yi da shugaban masu rinjayi a majalisar dattawa, Mitch McConnell da shugabannin majalisar wakilai a kan sabon tallafin na coronavirus bata yi wani tasiri ba.
“Haka bai cimma ruwa ba, amma dai akwai kwarin gwiwar samun haka,” inji Pelosi.
A jiya Juma’ar kuma, McConnell, dan Republican mai wakiltan Kentucky, ya shawarci majalisar dokoki da ta karkatar da dala biliyan 455 na ba kananan kasuwanci rance da ba a riga an kashe su ba zuwa ga taimakon COVID-19. Shawarar tasa ta biyo bayan ganawa da sakataren bitalmali Steven Mnunchin da kuma shugaban ma’aikatan fadar White House, Mark Meadows.
Psaki ya ce Biden da Pelosi da Schummer suna aiki tare a kan kudurin dokar tallafin annobar kafin majalisar dokoki da kammala aikinta na shekara.