Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin Mutune Miliyan 54 Suka Kamu Da COVID-19 a Duniya


Yankin Navajo a Amurka ya sanya matakan kulle tsawon makonni 3 saboda karuwar yaduwar cutar COVID-19.

Kusan mutane miliyan 54 ne suka kamu da cutar coronavirus a fadin duniya, a cewar rahoton cibiyar samar da bayanan coronavirus ta Johns Hopkins a yau Lahadi.

Amurka, India, da Brazil ne ke ci gaba da kasancewa kan gaba a matsayin wuraren da cutar ta fi kamari. Amurka na da kusan adadin mutun miliyan 11 da suka kamu da cutar, yayin da India ke da miliyan 8.8, Brazil kuma miliyan 5.8.

Ranar Lahadi 15 ga watan Nuwamba India ta sanar da samun mutun 41,100 da suka kamu da cutar cikin sa’o’I 24 da suka gabata.

Karuwar yaduwar cutar a Amurka ya sa yankin Navajo daukar matakan kulle tsawon makonni 3 daga ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG