Jiragen Saman Mali Sun Kashe Akalla Mutum 21 A Arewacin Kasar

Kanar Assimi Goita, Mali

Akalla mutum 21 da suka hada da kananan yara 11 ne suka mutu sakamakon wani harin da jiragen yaki mara matuka a ranar Lahadin da ta gabata a garin Tinzaouaten da ke arewacin kasar Mali, kusa da inda sojojin kasar suka yi mummunan rauni a watan da ya gabata, in ji 'yan tawayen Abzinawa

Tuni dai kasar Mali ta kai hare-hare ta sama kan maboyar 'yan ta da kayar baya a birnin Tinzaouaten da kewaye jim kadan bayan da Abzinawa da mayakan Islama suka kashe wani adadi mai yawa na sojojin Mali da sojojin haya na Wagner na Rasha a kusa da garin a cikin watan Yuli.

Garin da ke kusa da kan iyaka da Algeria, ya sake fuskantar wani hari da jirage marasa matuka a ranar Lahadin da ta gabata, in ji mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin 'yan tawaye da aka fi sani da Strategic Framework for Defence of the People of Azawad (CSP-DPA) a cikin wata sanarwa.

Hare-haren dai sun auna wani kantin magani da taron jama'a, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 21 na wucin gadi, ciki har da yara 11 da manajan kantin. Wasu da dama kuma sun jikkata kuma an samu barna mai tsanani.

Reuters