Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 21 A Wani Bikin Aure


Mali
Mali

Wata kungiya dauke da makamai ta kai hari a yayin wani bikin aure a tsakiyar kasar Mali tare da kashe akalla mutane 21, kamar yadda mazauna yankin suka fada a ranar Laraba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin sojojin kasar Afirka ta Yamma ke fafutukar yaki da tashe-tashen hankula daga masu tsattsauran ra'ayi.

Mali
Mali

Maharan sun kutsa kauyen Djiguibombo akan babura wanda ke garin Bandiagara a yammacin ranar Litinin din da ta gabata yayin da mazauna yankin ke bikin ma'auratan, a cewar Bakary Guindo, shugaban kungiyar matasan yankin.

"Yawancin wadanda abin ya shafa yankan rago aka musu" in ji Guindo.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai ya biyo bayan irin wanda kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta JNIM da ke da alaka da Al-Qaida ke kai hare-hare a yankin.

Mali
Mali

Al'umomi a tsakiyar kasar Mali da arewacin kasar sun shiga cikin irin wannan tashin hankali a shekara ta 2012.

An tilastawa 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayi sauka daga mulki a garuruwan arewacin kasar a shekara 2013, tare da taimakon sojojin Faransa da aka kora kwanan nan.

Masu tsattsauran ra'ayin dai sun sake haduwa tare da kaddamar da hare-hare kan kauyukan da ke nesa da jami'an tsaro.

Mali
Mali

Kusan shekaru hudu bayan kwace mulki da kuma ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen waje, har yanzu dai shugabannin sojojin Mali ba su samu nasarar dakile tashe-tashen hankula ba.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG