Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Arewacin Mali Sun Ce Sun Kwace Sansanin Sojoji


Mayakan kungiyar 'yan tawayen neman 'yancin Azawad ta 'yan kabilar Abzinawa a kasar Mali, zaune cikin motarsu a wata kasuwa dake Timbuktu a kasar Mali, a watan Afrilun 2012.
Mayakan kungiyar 'yan tawayen neman 'yancin Azawad ta 'yan kabilar Abzinawa a kasar Mali, zaune cikin motarsu a wata kasuwa dake Timbuktu a kasar Mali, a watan Afrilun 2012.

'Yan tawayen Abzinawa a arewacin Mali sun fada a ranar Laraba cewa, sun sake kwace wani sansanin soji daga hannun sojojin Mali, wanda ya kawo adadin sansanonin mamayar da aka yi wa kawanya zuwa biyar a makonnin da suka gabata.

Mohamed Elmaouloud Ramadane, mai magana da yawun kungiyar Azawad Movements (CMA), ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mayakansa sun karbe iko da sansanin sojojin Mali da ke Taoussa bayan fafatawa. Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga rundunar.

CMA dai kawance ce ta kungiyoyin 'yan tawaye da al'ummar Abzinawa masu ra'ayin mazan jiya na kasar Mali suka kafa, wadanda suka dade suna korafin rashin kulawa da gwamnati da kuma neman 'yancin cin gashin kai ga yankin hamadar da suka kira Azawad.

Kungiyar ta CMA ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin da ta gabata da kuma mayakan sa-kai masu goyon bayan gwamnati a shekarar 2015. To sai dai tashin hankali ya sake kunno kai tun bayan da sojoji suka hada karfi da karfe a juyin mulki guda biyu a shekarar 2020 da 2021, tare da wani dan kwangilar sojan Rasha na Wagner Group, inda su ka kori sojojin Faransa da kuma Sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD.

Harin na CMA a Taoussa ya biyo bayan harin da aka kai a sansanonin soji a Bamba, da Lere, da Dioura da Bourem a makonnin baya-bayan nan, duk a arewaci da tsakiyar kasar Mali inda bangarorin biyu ke neman mallakar yankuna.

Ramadane ya kuma ce, CMA ta kai wa sojojin hari a kusa da kauyen Tarkint ranar Laraba.

~ REUTERS

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG