TILABERY, NIGER - Hakan ya faru ne akan hanyarsu ta komawa gida bayan da suka sauke lodi a kasar Mali, lamarin da ke kara fayyace girman matsalar tsaro a yankin da ‘yan ta’adda ke cin karensu ba babbaka yau shekaru kusan goma.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 3 ga watan Maris na 2024 a tsakanin garin Ayorou dake Nijar da garin Lebzanga a kasar Mali, inda maharan wadanda ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne suka tare motocin dakon man akan hanyarsu ta dawowa gida, suka kuma kakkashe direbobi da yaransu kafin suka cinna wa motocin wuta kamar yadda babban magatakardan kungiyar direbobi ta SDRN Almou Yacouba ya yi wa Muryar Amurka bayani ta wayar tarho.
A yanzu haka shugabanin kungiyar direbobin da abin ya rutsa da su sun shiga yunkurin neman hanyoyin dauko gawawwakin wadanan mamata ta yadda za a yi musu jana’iza a gida.
Kawo yanzu ba wata sanarwa a hukumance dangane da wannan aika-aikar da ke wakana a wani lokacin da ake ganin alamun kura ta lafa ta bangaren da jihar Tilabery ke makwaftaka da yankin arewa maso gabashin Mali.
Matsalar tsaro na daga cikin dalilan da sojojin Nijar suka ayyana a jerin hujjojin da suka ce sun dogara kansu wajen kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna