Gamayyar jami'an 'yan sandan Najeriya da jami'an kare jama'a da ake kira Civil Defense ta kai ziyara a wasu makarantun jihar Borno, inda ta yi wa daliban alkawarin basu kariya ta musamman.
Jami'an tsaron sun ce irin abun da ya faru a makarantar mata dake Dapchi inda aka sace wasu 'yan mata ba zai sake faruwa ba cikin ikon Allah.
Jami'an tsaron sun hada da babban sifeton 'yan sandan Najeriya, da babban kwamandan Civil Defense, Alhaji Abdullahi Gana, wadanda suka zaga makarantu su na ba daliban kwarin gwuiwa saboda abun da ya faru a Dapchi.
Babban sifeton 'yan sandan wanda mataimakinsa ya wakilta ya yiwa daliban jawabi tare da cewa "mun zo ne domin mu karawa daliban kwarin gwuiwa game da batun tsaronsu saboda abun da ya faru a makarantar mata dake garin Dapchi kuma mun zo ne bisa umurnin shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari don mu tabbatar da cewa mun samar da tsaro a duk makarantun arewa maso gabas"
Ya kara da cewa ba zasu bari irin hakan ya sake faruwa ba inda za'a zo a kwashe dalibai haka kawai. Zasu ba duk makarantun jihohin tsaro.
Shi ma kwamandan Civil Defense Alhaji Abdullahi Gana ya yi karin haske game da ziyarar tasu inda ya ce duk jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe zasu basu tsaro. A cewarsa zasu tsara sunayen jami'an tsaro da zasu tura makarantun amma ya ki ya bayyana yadda zasu yi aikin sabili da dalilan tsaro.
A saurari rahoton Haruna da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5