Rundunar sojin saman Najeriya ta ce, ta tura karin jiragen sama a yankin arew maso gabashi da masu tattara bayanan sirri a kokarin gano inda aka boye ‘yan mata dalibai na makarantar Dapchi da aka sace a makon da ya gabata.
Jaridar Nation ta ruwaito cewa Darektan yada labarai na rundunar sojin sama ta Najeriya, Air Vice Marshal Olatokunbo Adensanya, ya yi kira ga jama’ar yankin da su taimaka da bayanai.
“Rundunar dakarun saman Najeriya, ta tura karin jiragen sama har da masu saukar ungulu domin kokarin gano ‘yan matan da suka bata.” Jaridar ta Nation ta ruwaito Adesanya yana fada.
Hakan na faruwa ne a daidai lokacon da gwamnatin Najeriyar ta fitar da adadin ‘yan matan da suka bata.
Gwamnatin ta ba da tabbacin cewa ‘yan matan sun kai 110.
Wannan adadi ya haura 105 da iyayen yaran suka fitar a baya, bayan binciken da suka gudanar na gashin kansu.
A jiya Lahadi ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana wannan adadi, yayin wata ziyara da ya kai Damaturu.
Ministan ya ce, gwamnatin na iya bakin kokarinta wajen ganin an kubutar da daliban kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
A ranar Litinin din da ta gabata, wasu 'yan bindaga da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka far garin Dapchi, inda ake zargin sun yi awon gaba da 'yan matan.
Saurarin tattaunawar Maryam Dauda da wakilinmu Haruna Dauda Biu kan halin da ake ciki dangane da batan 'yan matan na Dapchi:
Facebook Forum