Daruruwan malaman kwantiragi na kananan makarantun jamhuriyar Nijar suka fito domin gudanar da sallah da addu'o'i Allah ya kawo kwanciyar hankali a kasar da kuma biya masu bukatunsu.
Kawo yanzu gwamnatin Nijar ta kasa biyan albashinsu kan lokaci. Wasunsu sun yi sallar eidel fitr babu ko kwandala a hannunsu saboda ba'a biyasu ba. Wasu na tsoron za'a iya fiddasu daga gidajen haya.
Mai watsa labaran kungiyar malaman gefen mata Malama Maryama ta kara haske akan dalilin fitowarsu.Tace sun kirasu ne ganin yau 24 ga watan Yuli basu ji komi ba kamar yadda ba'a biyasu albashin watan Yuni ba duk da alkawarin da gwamnati tayi na biyansu kowace ranar takwas ga wata. Gashi yau 24 ga wata ba'a ce masu komi ba. Malaman ma suna jin kunyar bin wasu wurare saboda basukan da ake binsu.
Gwamnan jihar Malam Audu Mamman yace sun dauki matakin warware matsalolin malaman kwantiragi. Duk wanda bai samu albashinshi ba zai samu nan da zuwa Litinin. Ya rokesu su kara hakuri. Idan akwai kudi zasu samu amma idan an samu 'yar matsala kadan su gane su yi hakuri.Babu dadi a ce lokacin albashi ya kai ba'a biya ba.
Ga rahoton Shaaibu Mani.
Your browser doesn’t support HTML5