Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Har Yanzu Ana Tsare Da Musa Tchangari


Jami'an Tsaron Nijar
Jami'an Tsaron Nijar

A wani kamun da jami'an tsaron kasar Nijar suka yi wa wani dan jarida mai zaman kansa Malam Moussa Tchangari, Ministan sadarwar kasar Malam Yahuza Salisu ya ce doka na iya hawa kan kowa.

Jahar Difa jamhuriyar Nijar na cikin dokar ta baci tun halin da ta shiga ciki biyo bayan wasu hare haren da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai a wannan jaha wanda ya sa jama’ar jahar cikin wani mawuyacin hali musamman yadda a cikin irin wannan yanayi, jami’an tsaro ke da wuka da nama domin dukar wasu matakai na musamman domin tabbatar da doka da oda, da kuma kare al’uma baki daya.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, jami’an tsaro a Jahar ta Difa dake a jamhuriyar Nijar sun yi awon gaba da da wasu sarakunan gargajiya a yankin Difa wadanda ake zargin su da sa hannu kokuma alaka da kungiyar tada kayar bayan nan wadda aka sani da Boko Haram da ta dade tana kai hare hare iri iri a Najeriya da Nijar da Chadi.

Wadadan nan sarakai kamar yadda ma'aikacin muryar Amurka Abdul'aziz Adili Toro yayi hira da Ministan Sadarwar kasar Nijar Malam Yahuza Salisu, ya bayyana cewar ba'a tabbatar da zargin da ake yi masu ba amma ana cigaba da bincike akan su.

A cewar Ministan "doka ta kowa ce kuma hukuma ce kdai zata bincika sannan ta yanke hukunci."

Daga karshe ya kara da cewar "kamau da jami'an tsaro suka yi wa Moussa Tchangari duk cikin doka ce, kuma doka tana iya hawa kan kowa. jami'an tsaron nan suna da nasu dalili kuma tambayoyi suke yi kuma suna da hujjojin su na yin haka."

Nijar: Har Yanzu Ana Tsare Da Musa Tchangari - 3'01"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG