Hakan ya hada da dubban masu fafutukar adawa da yaki wadanda suka shirya yin zanga-zanga a kusa da dandalin taron na Democrat inda Mataimakiyar Shugaban kasa Kamala Harris za ta amince da zabin da jam’iyyar ta yi mata a matsayin ‘yar takarar shugabar kasa.
A farkon wannan watan ne, wakilai suka tsayar da Harris a matsayin wadda za su zaba.
Kowace rana cikin kwanaki uku da za a kwashe ana taron na da takenta. Taken Litinin shi ne “domin al’uma, domin makomarmu.”
Ana sa ran Uwar gidan shugaban kasa Jill Biden da mijinta Shugaba Joe Biden da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary na daga cikin wadanda za su gabatar da jawabinsu a daren Litinin.
Yayin da 'yan jam'iyyar Democrat ke fara babban taronsu a birnin na Chicago, yakin neman zaben Donald Trump na kokarin dawo da martabarsa bayan kwashe makonni yana kokarin samun daidaito bayan da Harris ta zama ita ce ‘yar takarar shugaban kasar jam’iyyar.
Trump zai yi kokarin kassara taron na ‘yan Demcorat da tarukan da za a cika makil a jihohin da ake kare-jini-biri-jini inda zai tallata manufofinsa.
Wannan ne makon yakin neman zabensa da yake da abubuwan da zai yi da yawa tun bayan lokacin hunturu inda ya fafata da abokanan hamayyarsa na ‘yan Republican.