Jami’an yakin neman zabenta da kawayenta sun yi ta kiraye-kiraye a madadin Harris a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka bukaci wakilan jam’iyyar Democrat da za su halarci babban taron jam’iyyar Democrat a wata mai zuwa da su hada kai wajen tsayar da ita takarar shugaban kasa a zaben da za a yi a ranar 5 ga watan Nuwamba da Donald Trump na Republican.
Majiyoyi da dama sun ce kiraye-kirayen da mukarrabanta suka yi mataki ne na shan gaban masu sha'awar yin takara da ita a jam'iyyar ta Democrat bayan da Biden mai shekaru 81 ya janye takararsa.
A lokaci guda, shugabannin jam'iyyar Democrat a jihohi sun goyi bayan Harris a wani kiran waya, a cewar majiyoyi da dama.
Takarar Harris, mai shekaru 59 wacce bakar fata ce kuma Ba'amurkia ‘yar asalin Asiya, za ta bude wani sabon babi inda za ta kara da Trump, mai shekaru 78, wanda suka fito daga mabanbantan rukkunan shekaru da ala'du.
Har yanzu dai Amurka ba ta taba zaben mace a matsayin shugabar kasa ba a tarihinta na shekaru 248.
"Harris za ta fi saukin kayarwa akan Joe Biden," Trump ya fadawa CNN jim kadan bayan sanarwar Biden.
Biden, wanda shi ne mutum mafi tsufa da ya taba rike mukamin shugaban kasa, ya ce zai ci gaba da kasancewa a mukaminsa har sai wa'adinsa ya kare a ranar 20 ga Janairu, 2025, yayin da ya amince Harris ta tsaya takarar shugaban kasa a madadinsa.
Fadar White House ta ce Harris za ta gabatar da jawabi a farfajiyar Fadar White House da karfe 11:30 na safe (agogon gabashin Amurka) a ranar Litinin a wani taron taya kungiyoyin da suka lashe gasar zakarun koleji ta NCAA 2023-24.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna