Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitaccen Tarihin Tim Walz


Tim Walz
Tim Walz

An sake zaben Walz a wa’adi na biyu a shekarar 2022 a jihar ta Minessota bayan da ya doke dan takarar jam'iyyar Republican Scott Jensen.

An haifi Gwamna Tim James Walz a West Point da ke jihar Nebraska, wata unguwa mai mazauna 3,500 a arewa maso yammacin Omaza a ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 1964.

Walz ya shiga aikin soja inda ya zama malami a jihar ta Nebraska.

Ya kwashe shekaru 24 yana aikin na soja kafin daga bisani ya yi ritaya a shekarar 2005 inda ya fita da mukamin Sergeant Major.

Walz ya taba horar da 'yan wasan kwallo a wata makaranta da ke Gundumar Mankato.

Bayan da ya shiga harkar siyasa, Walz ya yi wa’adi shida a Majalisar Wakilan Amurka inda ya yi ta fafutukar kare hakkokin tsoffin sojin kasar.

A lokacin da Gwamna Mark Dayton na jam’iyyar Democrat ya yanke shawarar ba zai sake neman wani wa’adi ba a shekarar 2018, Walz ya karbi ragamar inda ya lashe zabe karkashin taken “hada kan jama’ar Minnesota.”

An sake zaben Walz a wa’adi na biyu a shekarar 2022 a jihar ta Minessota bayan da ya doke dan takarar jam'iyyar Republican Scott Jensen.

Har yanzu Walz shi ne gwamnan jihar ta Minnesota. Shi ne Gwamna na 41 a jerin gwamnonin da suka mulki jihar.

‘Yan Republican kan caccaki Walz kan yadda ya ja kafa wajen dakile tarzomar da ta barke bayan da ‘yan sanda suka kashe George Floyd a shekarar 2020.

A shekarar 1994 Walz ya auri matarsa Gwen, yana kuma da ‘ya’ya biyu.

A ranar 6 ga watan Agustan 2024, Harris ta zabi Walz a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban kasa a zaben 2024.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG