Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Republican Za Su Fuskanci Manufofin Harkokin Waje A Babban Taronsu Na Daren Yau


Taron 'Yan Republican Na AMurka
Taron 'Yan Republican Na AMurka

Kwana na 3 na babban taron jam’iyyar Republican zai soma a daren yau Laraba karkashin jagoranci hadakar Donald Trump da JD Vance da aka zaba a baya-bayan nan zasu maida hankalinsu kan batutuwan da suka shafi tsaron kasa da manufofin kasashen ketare.

Ana sa ran ‘yan Republican din su maida hankali akan yadda Shugaba Joe Biden na jam’iyyar Democrat yake gudanar da rikice-rikicen da ake fama dasu a nahiyar Turai da yankin Gabas ta Tsakiya.

Ana sa ran tsaffin jami’an gwamnatin tsohuwar gwamnatin Trump su fito su bayyana yadda manufar kasashen ketaren za ta kasance a gwamnatin Trump ta 2.

Me yiyuwa hakan ta hada da jawabai daga mutane irinsu Richard Grenell, tsohon daraktan riko a hukumar leken asirin Amurka karkashin tsohuwar gwamnatin Trump, da kuma sakataren harkokin wajen Amurkan Mike Pompeo.

Haka kuma ana sa ran Vance ya amince da zabin da aka yi mishi na zama mataimakin shugaban kasa.

Har ila yau, da dama daga cikin jawaban da za’a gabatar a daren yau Laraba zasu maida hankali ne akan yadda gwamnatin shugaba Biden ke gudanar da al’amuran duniya, ciki harda batun yadda Amurka ta janye daga Afghanistan cikin rudani da yakin da ake fafatawa tsakanin Isra’ila da Hamas, a cewar kwamitocin yakin neman zaben Trump da na jam’iyyar Republican mai taken “sake dawowa Amurka da karfinta” wato Make America Great Again a turance.

JD Vance, hagu, Trump, dama
JD Vance, hagu, Trump, dama

‘Yan Republican na kallon batun manufar kasashen ketare a matsayin jigon batutuwan da zasu yi yakin neman zabe akai, inda suke cewar matsayar Amurka a idon duniya yafi kima a zamanin mulkin Trump duk da karuwar yunkurin zama saniyar waren da jam’iyyar ke yi.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG