Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyar Republican Ta Tsayar Da Donald Trump Takarar Shugaban Kasa Karo Na Uku


Donald Trump
Donald Trump

Jam'iyar Republican ta tsayar da tsohon Shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin dan takararta a zaben Shugaban kasar da za a gudanar a watan Nuwamba wannan shekarar.

Kwanaki biyar bayan ya tsallake rijiya da baya daga yunkurin halaka shi, Shugaba Donald Trump dauke da bandeji a jikin shi yayi jawabi ga babban taron kasa na jam’iyar Republican a ranar Alhamis, inda ya karbi zaben da aka yi mishi na dan takarar shugaban kasa, ya kuma gabatar da jawabin da ya fuskanci batun hadin kan jam’iyar shi da kuma hadin kan kasa, a fafutukar da ya ke yi na neman shiga fadar white House a karo na uku.

Tsohon shugaban mai shekaru 78 a duniya, da yayi fice wajen caccakar abokan hamayarsa na siyasa a jam’iyun, yayi alkawarin sakon tausasawa bisa radin kan shi kan hadin kai, bayan da tsallake rijiya da baya.

Jawabin na Trump shi ya kai ga cikar karshen gagarumin taron gangamin kwanaki hudu da jam’iyar ta Republican ta gudanar da ya tattaro dubban 'yan fafutukar masu ra’ayin 'yan mazan jiya da zababbun jami’ai zuwa jihar raba gaddama ta Wisconsin, yayin da masu kada kuri’a ke jinjina yadda za su kada kuri’ar su a zaben da zai gabatar da yan takara biyu da basu da wani farin jinin azo a gani. To sai dai a kasa da watanni hudun da su ka rage aje ga takarar, manyan sauye sauye na iya faruwa a takarar, ko ma ace da wuya hakan bai faru ba.

Bayyanar ta Trump ta zo a lokacin da Shugaban kasa dan Democrat Joe Biden ke fafutukar neman ganin jam’iyar shi ta tsaida shi takara, a dai dai lokacin da ake kara samun matsin lamba da ga manyan abokan tafiya a majalisar dokokin kasar, da ma su bada gudummuwa, har ma da tsohon shugaba Barak Obama, wanda ya nuna fargaba kan mai yuwuwa ya gaza sake yin nasara a zabe bayan rashin katabus din shi a muhawarar da aka yi.

An dauki tsawon lokaci abokan hulda na matsa ma shuga Biden da ya aza kaimi a yakin neman zaben shi. Maimakon hakan, ya sami kan shi ne a kadaice a gidan shin a gefen ruwa a Delaware, bayan gwaji ya tabbatar da ya kamu da cutar COVID-19.

A yayin da Trump da aka sani da furta duk abin da ya fito daga bakin shi, yayi alkawari cikin lallausan lafazi a daren Alhamis, maganganun da aka shirya a ranar karshe ta babban taron, an tsara fitar da nuna karfin rauni akan Biden.Shirin ya dabbaku akan karfin kunji fiye da yadda ya kasance a ranakun makon.

Gigga giggan wadanda su ka yi jawabi sun hada da shahararren dan kokawar nan Hulk Hogan, shugaban zakarun yan dambe Dana White, da tsohon mai gabatar da shirye shirye a kafar talbijin din Fox News, Tucker Carlson. Kid Rock shine mawakin da ya cashe a wurin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG