Jakadan Kasar Turkiyya Ya Bukaci A Kulle Makarantun Kasar Dake Najeriya

Mataimakin shugaban jami’ar Turkish Nile University dake Abuja farfesa Hussaini ya nuna rashin jin dadinsa akan kiran da jakadan Turkiyya yayi wa mahukuntan Najeriya cewar su rurrufe dukkan makarantun kasar Turkiyyar dake najeriya.

Mataimakin shugaban ya bayyana cewa makarantun nasu na kiyaye dukkan dokokin Najeriya sau da kafa, kuma hukumar jami’o’in Najeriya ta amince dasu duk da cewa suna da fasfo din kasar Turkiyya, ya kuma kara da cewa babu wanda zai yi masu katsalanda cikin ayyukan su daga wata kasa, domin a cewar sa, jami’a ce ta kasa da kasa haka kuma daliban.

A bangaren iyayen daliban makarantar kuma, Suleman Uba Gaya mataimakin shugaba editoci na Najeriya ya bayyana cewa yana da ‘ya’ya dake karatu a irin wadannan makarantu, domin haka ya ce a tsawon shekarun da makarantun suka kwashe a Najeriya bai ga wani abin da zai sa haka kawai saboda dalilan siyasa jakadan Turkiyya ko gwamnatin kasar zata sa a rufe makarantun da ke samar da alheri ga Najeriya ba.

Kawo yanzu dai ba’a sami jin ta bakin gwamnatin tarayya ba, koda shike kakakin shugaban Najeriya Malam Muhammadu Shehu, da ministan yada labarai na kasar Alhaji Lai Muhammed sun bayyana cewa lamari ne daya shafi huldar diplomasiyya.

Ga cikakken rahoton a nan.

Your browser doesn’t support HTML5

Jakadan Kasar Turkiyya Ya Bukaci A Kulle Makarantun Kasar Dake Najeriya