Matsalolin dake faruwa a tsakanin masu goyawa kungiyar kwallon kafa ta Najeriya baya sun kaiga haifar da cafke daya daga cikin su a ofishin jakadancin kasar Brazil dake jihar Legas a Najeriya.
Jiya talata ne mai magana da yawun kungiyar Mr Hafeez Balogun ya fadawa manema labarai a birnin Legas cewa jami’an ‘yan sanda sun kama wata daga cikin mambobin kungiyar, matar wadda aka kama taje ofishin jakadancin da sunan tsohon shugaban kungiyar da aka tsige ne da takardun bayanan bogi.
Ya kara da cewa takardun bogin na izinin shiga kasar ta Brazil na ‘yan kungiyar ne wadanda zasu je goyon bayan kungiyar a wasannin motsa jiki na Olympics da za’a fara ranar 5, ga watan Agustan wannan shekarar na Rio Dejaneiro a kasar Brazil.
Ofishin jakadancin ya tabbatar da cewa yawancin bayanan ‘yan kungiyar da tsohon shugaban da aka tsige ya bayar na bogi ne musamman ma bayanansu na bankuna. Jami’an ofishin jakadancin sun yi barazanar kiran jami’an ‘yan sanda idan ba’a janye takardun bayanan ba amma suka ki, a cewar Mr Balogun.
Daga karshe ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi awon gaba da matar wadda aka sakaya sunanta, kuma yanzu haka daya matar da suka je ofishin tare da tsohon shugaban da aka tsige na ci gaba da boyo domin gujewa kamun jami’an ‘yan sanda