Isra’ila Da Hamas Sun Amince Da Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta

ISRAEL-PALESTINIANS/YARJEJENIYA

Ana sa ran sabuwar yarjejeniyar za ta kubutar da karin wasu mutane da aka yi garkuwa da su daga Gaza, yayin da Isra’ila za ta saki karin wasu Falasdinawa.

Gwamnatin Qatar ta sanar a ranar Litinin cewa Isra’ila da Hamas sun cimma matsaya kan tsawaita yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Zirin Gaza da tsawon kwanaki biyu.

Hakan na faruwa ne yayin da mayakan suka sake sakin wadanda suka yi garkuwa da su, sanna gwamnatin Yahudawa ta saki wasu karin fursinonin Falasdinawa.

Kasar Qatar ce ta shiga tsakanin na tsawaita bude wuta na wucin gadi, kuma ya zo ne a rana ta karshe na ainihin yarjejeniyar kwanaki hudu na dakatar da bude wuta tsakanin bangarorin biyu da ba sa ga maciji.

Amurka, wadda ta yi ta kira da a dakatar da bude wuta muddin ana sako mutanen da aka yi garkuwa da su, ta ce ta yi maraba da tsawaita wa’adin da aka yi a fadan.

Shugaban Amurka Joe Biden ya fada a cikin wata sanarwa da aka fitar cewa dakatar da yakin, zai ba da damar karin taimakon jin-kai ga fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba, wadanda ke shan wahala a fadin Zirin Gaza.

Ya ce Amurka ba za ta dakatar da kokarinta na diflomasiyya ba har sai an sako dukkan mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

Isra’ila ta ce za ta dakatar da mamaya ta kasa da kuma kai hare-hare ta sama a kan Hamas a Zirin Gaza da kwana daya, bayan yarjejeniyar da aka kulla ta farko ga duk wasu mutane 10 da Hamas za ta saki tare da sakin ninki uku na Falasdinawa da take rike da su a gidajen yarin Isra’ila kan laifuka daban-daban.

Hamas ta tabbatar da cewa ta amince da wa’adin dakatar da bude wuta na kwanaki biyu, a karkashin wannan sharudda.

Da yammacin ranar Litinin ne dai aka fara musaya ta hudu na wadanda aka yi garkuwa da su da Hamsa ke rike da su da fursunonin Falasdinawa, inda rundunar tsaron Isra’ila ta ce an sako wasu mutane 11 da Hamas ta yi garkuwa da su, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Isra’ila.

Cikin kwanaki hudu da suka gabata, an sako jimullar ‘yan Isra’ila 50 da aka yi garkuwa da su, sannan ana sa ran sakin Falasdinawa 150.