Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Isra'ila-Hamas Ta Fara Aiki


Wata mata zaune a kusa da gidanta da aka lalata a yankin Gaza
Wata mata zaune a kusa da gidanta da aka lalata a yankin Gaza

A ranar Juma'a ake sa ran sako mutum 13 da aka yi garkuwa da su a Gaza, kuma za’a saki karin wasu rukunin wadanda aka yi garkuwa da su a kowace rana na dakatar bude wuta har sai an sako jimullar mutum 50. 

A ranar Juma’a yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Isra’ila da Hamas ta fara aiki da misalin karfe 7 na safe agogon yankin wato karfe 5 agogon GMT.

An tsara za’a sako rukunin farko na mutanen da aka yi garkuwa da su daga Gaza da misalin karfe 4 na yamma, a cewar ma’aikatar harkokin wajen Qatar, wacce ke taimakawa wajen tattauna wa a yarjejeniyar.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar Majed Al – Ansari, ya shaida wa manema labarai cewa, yarjejeniyar ta farko tun bayan fara yakin a watan da ya wuce, za ta hada da dakatar da bude wuta a arewaci da kudancin Gaza.

Dakarun Isra'ila
Dakarun Isra'ila

Karkashin wannan yarjejeniyar, za’a sako mata da yara kanana 50 da mayakan Hamas suka yi gaarkuwa da su daga Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, a madadin mata da kanana yara Falasdinawa 150 da aka daure a gidan yari da ke Isra’ila.

A yau Juma’a za’a sako mutum 13 da aka yi garkuwa da su a Gaza, kuma za’a saki Karin wasu rukunin wadanda aka yi garkuwa da su a kowace rana na tsagaita bude wuta har sai an sako jimullar mutum 50.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG