Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Saki ‘Yan Isra’ila 24 Yayin Da Isra’ila Ta Saki Falasdinawa 39


A convoy of vehicles carrying hostages abducted by Hamas militants during the October 7 attack on Israel arrives through the border crossing with Gaza
A convoy of vehicles carrying hostages abducted by Hamas militants during the October 7 attack on Israel arrives through the border crossing with Gaza

Bayan musayar rukunin farko na fursunoni tsakanin Isra'ila da Hama, kimanin manyan motoci 150 sun ketara zuwa Gaza dauke da kayan agaji da safiyar ranar Juma'a.

A yammacin ranar Juma’a ne aka sako mutane 24 da suka hada da mata da kananan yara 13 ‘yan Isra'ila, da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a wani hari da ba a taba ganin irinsa ba a Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

A halin da ake ciki, gwamnatin Isra'ila ita kuma ta saki mata Falasdinawa da maza matasa 39 aka daure ko kuma aka tsare a Isra’ila.

"Tawagar kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa da ake kira ICRC a takaice, a ranar Juma'a ta fara wasu ayyuka na tsawon kwanaki da yawa don taimakawa wajen ganin an sako, tare da kai mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma Falasdinawan da aka tsare a Isra'ila Yamma da kogin Jordan. Aikin zai hada da kai karin kayan agajin jinkai da ake bukata sosai zuwa Gaza,” a cewar hukumar ICRC a cikin wata sanarwa a kan yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwanaki hudu da Qatar ta taimaka aka cimma. Yarjejeniyar ta ba da damar musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas da kuma barin muhimman kayan agajin jinkai su shiga Gaza.

'Yar Falasdinu da Isra'ila ta sako.
'Yar Falasdinu da Isra'ila ta sako.

Bayan mata da yara ‘yan Isra'ila, kungiyar Hamas ta kuma sako 'yan kasar Thailand 10 da wani dan kasar Philippines wadanda ta yi garkuwa da su a cewar gwamnatin Qatar.

Isra'ila ta ce kimanin mutane 240 ne Hamas ta yi garkuwa da su a harin na ranar 7 ga watan Oktoba.

"An tura tankokin mai guda hudu da tankokin iskar gas guda hudu daga Masar zuwa ga kungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya da ke kudancin zirin Gaza ta mashigar Rafah," a cewar rundunar tsaron Isra'ila.

motocin kayan agaji
motocin kayan agaji

Kimanin manyan motoci 150 ne suka tsallaka zuwa Gaza dauke da kayan agaji daga safiyar Juma'a, a cewar kafafen yada labarai.

Kafin barkewar yakin tsakanin Isra'ila da Hamas, motoci kusan 500 ke shiga cikin yankin Falasdinu a duk rana.

Ana sa ran za a saki rukuni na biyu na ‘yan Isra’ila da aka yi garkuwa da su ranar Asabar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG