Tashe-tashen hankula a yammacin kogin Jordan sun yi kamari a cikin 'yan makwanni, tun bayan da Hamas ta kai wa Isra'ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba, inda ta kaddamar da wani mummunan yaki a zirin Gaza.
Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa da dama tare da kame daruruwan mutane a yammacin gabar kogin Jordan. Yahudawan mazauna Yammacin Kogin Jordan su ma sun kara kaimi a hare-hare.
Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana cewa, an kashe Falasdinawa biyar a sansanin Hamas na Jenin, yayin da wasu uku kuma aka kashe su a yankuna daban-daban na yammacin gabar kogin Jordan a safiyar Asabar. Daya daga cikin wadanda aka kashe a al-Bireh da ke tsakiyar gabar yammacin kogin Jordan, matashi ne, in ji ma'aikatar.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kashe Falasdinawa biyar a wani artabu da suka yi da su a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin, inda ta kama wani Bafalasdine da ake zargi da kashe wani uba da dansa na Isra'ila a wani wurin wankin mota a gabar yammacin kogin Jordan a farkon shekara.
Sojojin sun ce wadanda aka kashe mayakan ne. Kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu ta dauki daya daga cikin mutanen, mai suna Asaad al-Damj, mai shekaru 33 a matsayin mamba, yayin da sauran ba'a kai ga alakanta su da kungiyoyin 'yan ta'adda ba.
Rundunar sojin ta fada ba tare da wani karin bayani ba, cewa tana samun goyon bayan sojojin sama ne da suka kai hari tare da jikkata wadanda ta ce Falasdinawa ne masu dauke da makamai.
Rundunar ta kuma ce tana duba rahotannin sauran abubuwan da suka faru.
Dandalin Mu Tattauna