Sako mutanen da aka yi garkuwa da su karo na uku ya biyo bayan yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki hudun da aka yi ne.
Sanarwar da ofishin dake bibiyar al'amuran wadanda aka yi garkuwa da su da wandanda suka bata ta fitar, ta ce jami’an tsaro suna nan suna tantance sunayen da iyalan wadanda ake garkuwa da 'ya‘yan su suka tabbatar.
A halin da ke ciki dai, ma’aikatar kiwon lafiyar Falasdinu ta fada a yau Lahai cewa sojojin Isra’ila sun harbe wasu Falasdinawa su shida har lahira cikin dare a yammacin kogin Jordan.
sannan a wani bangaren kuma, Hamas ta sako wasu mutane 17 da take garkuwa da su da yammacin jiya Asabar, 13 daga cikin su Isra’ilawa da kuma ‘yan kasar Thailand hudu (4). Jim kadan bayan haka, da sanyin safiyar yau Lahadi, ita ma Isra'ila ta sako fursunoni 'yan Falasdinu 39.
Dandalin Mu Tattauna