Iraki Ta Haramta Wa Wasu Bankunan Kasar 8 Hada-Hada Da Dalar Amurka

Babban bankin Iraqi

Wata takardar babban bankin kasar da wani jami’i a bankin ya tabbatar da sahihancinta ce ta bayyana sunayen bankunan da aka haramtawa amfani da dalar.

Kasar Iraqi ta haramtawa bankunan kasar 8 yin hada-hada da dalar Amurka, a matsayin matakin rage damfara, hallata kudaden haram da sauran wasu hanyoyi da ake amfani da dalar Amurka don yin abubuwan da suka saba doka, wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan ziyarar da wani babban jami’in baitulmalin Amurka ya kai.

An haramtawa bankunan damar samun dala a saukake a duk rana daga babban bankin Iraqi, babbar hanyar samun kudaden kasar waje a kasar da ta dogara ga shigo da kayayyaki daga waje, wadda kuma Amurka ke sa wa ido a kokarin ta na magance safarar kudade zuwa makwabciyar kasar Iran.

Kasar Iraqi, da ke zaman abokiyar hulda ga Amurka da Iran, wadda ke da kudi fiye da dalar Amurka biliyan 100 ajiye a Amurka, ta dogara sosai ga taimakon Amurka domin tabbatar da ganin ba a toshe mata kudade da hanyar samun kudin shiga daga saida man ta ba.

Wata takardar babban bankin kasar da wani jami’i a bankin ya tabbatar da sahihancinta ce ta bayyana sunayen bankunan da aka haramtawa amfani da dalar.

Shugaban kungiyar bankuna masu zaman kansu na Iraki, wanda ke wakiltar bankunan da abin ya shafa, da bankunan Ashur da Hammurabi, nan take basu amsa bukatar su maida martani ba.

Wani mai magana da yawun baitulmalin ya ce: "Mun yaba da yadda babban bankin Iraki ke ci gaba da daukar matakai don kare tsarin hada-hadar kudi na kasar daga masu muzanta shi."

A watan Yulin shekarar 2023, Iraki ta haramta wa bankuna 14 gudanar da hada-hadar dala a matsayin wani bangare na yaki da safarar dala zuwa Iran ta hanyar bankunan Iraki. An dauki matakin ne bayan wata bukata daga Amurka, a cewar jami'an Iraqi da na Amurka.