Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kara Yawan Mai Da Ake Hakowa Zai Taimaka Wajen Farfado Da Naira - Masana


Faduwar darajar Naira
Faduwar darajar Naira

Matsalar faduwar darajar kudin naira abu ne da ya kara ta’azzara musamman a makonnin bayan-bayan nan inda ake sayen dala daya a kan naira 995 zuwa dubu 1 da 100 kasancewar karancin dala a cikin Najeriya.

A yayin da karancin dala da kuma faduwar darajar Naira ke kara ta'azzara, da matsalar karancin man fetur a sassan Najeriya daban-daban musamman ma manyan birane da suka hada da Legas, Abuja, fatakwal da dai sauransu, masana tattalin arziki da wasu ‘yan kasar sun ce mafita ga wannan matsala shi ne, gwamnati ta tashi tsaye wajen samar da wasu hanyoyin samun dala, da kara yawan danyen man da ake hakowa a cikin kasar, tabbatar da cewa matatar man Dangote ta fara aiki da kuma farfado da matatun man kasar da dai sauransu.

Matsalar faduwar darajar kudin naira abu ne da ya kara ta’azzara musamman a makwnnin bayan-bayan nan inda ake sayen dala daya a kan naira 995 zuwa dubu 1 da 100, kasancewar karancin dala a cikin Najeriya lamarin da ke jawo hauhawar farashin kayayyakin masarufi da sauran ababen amfanin gida na yau da kullum kamar yadda Mal. Aminu Abbas Gumel ya shaida mana.

Alkaluma sun yi nuni da cewa faduwar darajar naira na shafar kusan dukkan ‘yan Najeriya kama daga kanana da manyan ‘yan kasuwa, dillalan man fetur, dalibai da ke karatu a cikin gida da ma wajen kasar, ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kan su da dai sauransu

A yanzu dai ana sayen dala 1 a kan Naira 1,100 sama a kasuwannin bayan fage, sabanin farashin da ke shafin yanar gizon babban bankin Najeriya na naira 883 da kwabo 56 a hukumance, lamarin da masana tattalin arziki a kasar ke ganin cewa wani sabon koma-baya ne ga al’ummar da ke cikin matsin rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi a watan Mayun shekarar nan.

A yayin da wasu ‘yan Najeriya ke alakanta dogayen layukan da aka fara gani a gidajen mai a manyan biranen kasar da rashin wadatattun kudaden dala a cikin kasar, wasu kuma na zargin cewa wasu dillalan mai ke boye mai don kuntatawa talakawa.

Malam Kasim Garba Kurfi, masanin tattalin arziki ne a Najeriya, ya ce faduwar darajar naira bai zo da mamaki ba kasancewar halin kaka-ni-kayin da ake ciki tun bayan cire tallafin man fetur ba tare da sanya matakan rage radaddin da hakan zai kawo ba.

Ya kara da cewa mafita shi ne kara yawan danyen man da ake hakowa a cikin kasar, tabbatar da cewa matatar man Dangote ta fara aiki da kuma farfado da matatun man kasar da dai sauransu.

Wasu masana dai na ganin cewa faduwar darajar naira bai rasa nasaba da dage takunkumin da babban bankin kasar ya yi a kan wasu kayayyakin da aka haramta shigowa da su cikin kasar tun shekarar 2015 a ranar 12 ga watan Oktoban nan da muke ciki.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG