Kungiyar 'yan canjin ta dauki matakin yajin ne don nuna ba ta da hannu wajen tashin gauron zabin da dala ke yi har ta kai Naira 1,500 kan dala daya.
Yajin ya sanya masu son canja dala da su ka hada da ma'aikatan kungiyoyi masu samun dauki daga ketare da 'yan diflomasiyya shiga halin damuwa.
A hirar shi da Muryar Amurka, Shugaban kungiyar 'yan canjin Alhaji Abubakar Aabdullahi Dauran ya ce yajin na su ya cimma muradun sa don haka sun janye.
"A jumma'ar nan za mu dawo aiki don sakon da mu ke son isarwa gwamnati cewa ba mu da hannu a tashin dala ya isa inda ya dace. Mu na tausayawa 'yan Najeriya don mu ma kasuwa daya da su mu ke shiga mu sayi kaya."
Sakataren kungiyar 'yan canjin Alhaji Abubakar Muhammad ya aza alhakin tashin farashin kan wasu shafukan dillalan canji na yanar gzio, Ya kara da cewa, 'mu na son gwamnati ta dauki matakin rufe shafukan don galibinsu suna aiki ne daga kasar China."
Nan da can dai wasu matasa 'yan canjin na nuna ba za su bar canjin ba don samun na kalaci.
Kasuwar da ke anguwar ZONE 4 a Abuja na da akalla mutum na kai tsaye da bayan fage da su ka kai 20,000 da ke cin gajiyar hada-hadar ta kudin ketare.
Jami’an EFCC a baya kan kai samame kasuwar da hakan kan haddasa zaman doya da manja tsakanin su da ‘yan kasuwar.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna