Dillalan sun bayyana haka ne a sanarwar da suka fitar ta bakin mai hulda da jama'a, a ƙungiyar, Chinedu Ukadike, inda ya ce farashin man-fetur zai ƙara tashi daga matsayin da ya ke a yanzu, bisa irin hauhawar da dalar Amurka ke yi.
Ya ƙara da cewa, da zarar farashin dalar Amurka ya hau, kai tsaye hakan yake shafar farashin man-tetur din da su ke shigowa dashi da kuma dangoginsa.
Baya ga nan, Chinedu Ukadike ya ce farashin gangar danyan mai shi ma ya tashi a kasuwa, wanda hakan kuma dole zai shafi farashin na man-fetur.
Chinedu, ya ce "yanzu haka ana siyan litar man-fetur akan farashin Naira 617 ko kuma Naira 596, ya danganta da nisan inda mutum yake siya, wannan farashi ba zai ci gaba da zama a haka ba, saboda farashin dalar Amurka da kuma gangar man-fetur duk sun tashi"
A hirarsa da Muryar Amurka, babban mai kula a ƙungiyar ta IPMAN, Yakubu Ali Bulkadimka, ya ce haka zalika farashin na man-fetur zai tashi, saboda farashin man dizel ya ƙaru, kuma da shi suke jigilar man-fetur zuwa sassan Najeriya, baya ga haka, ya ce har yanzu Gwamnati ba ta biya su kuɗin jigilar da suke binta ba.
Su ma sauran masu gidajen mai sun koka, bisa wannan sabon farashin man-fetur da ke tunkararsu, kamar yadda Rabe Musa, ɗaya daga cikin masu gidajen man-fetur, ya shaida wa Muryar Amurka.
Duk ƙoƙarin jin ta bakin hukumar da ke kula da sha'anin man-fetur na ƙasa wato NMDPRA, ya ci tura.
Saurari rahoton Ruƙayya Basha:
Dandalin Mu Tattauna