Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Bayyana Mabambantan Ra’ayoyi Kan Faduwar Darajar Naira


Kudin naira
Kudin naira

Bankin Duniya ya wallafa wani rahoto da ke cewa tun daga tsakiyar watan Yuni na shekarar 2023 darajar Naira ta ragu da kashi 40 cikin 100. Wannan ya nuna cewa naira ta zama kudi mafi lalacewa a cikin kudaden da ake kasuwanci da su a kasashen Afirka. Masana sun tofa albarkacin bakinsu.

Bankin duniya ya nuna cewa faduwar darajar Naira ya samo asali ne daga matakin da Babban Bankin kasar ya dauka na cire takunkumin kasuwanci a kasuwannin Gwamnati, abin da ya nuna cewa daidaiton farashin kasuwannin musayar kudi ya kara matsalolin hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

Rahoton ya ce Naira ta fadi daga 473.83 a matsayin canjin dala daya, zuwa kimanin Naira 800 a canjin dala daya a hukumance.

A cewar Bankin Duniya, a watan Maris na shekarar 2020 zuwa watan Yunin shekarar 2023 ne aka ga bambancin da ke tsakanin daidaiton da farashin canjin Naira ya samu a hukumance, abin da ya sa kwararre a fannin tattalin arziki na kasa da kasa, Shu'aibu Idris Mikati fadin cewa rahoton ya zo masa da mamaki.

Mikati ya ce idan an bibiyi maganganun da hukumar lamuni ta duniya da bankin duniya suke fitarwa a game da yadda ake hada-hadar cinikayya da kasashen ketare, ya kamata a tuna cewa su kansu sukan matsa a daina samun kasuwa kala biyu, wato kenan a ce akwai kasuwa ta Gwamnati da kuma ta gefe.

Mikati ya kara da cewa a yanzu an samu Gwamnatin da ta zo ta fitar da farashin dala bai daya, sai kuma su fito da bayanin cewa Naira tana cikin kudaden nahiyar Afirka da darajarta ta fadi warwas, ba daidai ba ne a cewarsa, domin da bankin duniya ya bincika sosai zai ga cewa darajar kudin Sudan ta fadi har da kashi 77 cikin 100 a cikin wannan dan tsakanin, haka kuma na kasar Somalia.

Shi ma malami a Jami'ar Kashere ta Jihar Gombe, kuma kwararre a fannin tattalin arziki Dakta Isa Abdullahi, ya yi tsokacin cewa Najeriya ta shiga wata ukuba wajen canjin kudi kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana, wannan ya nuna cewa idan an kwatanta naira da kudaden kasashe irinsu Cedi na Ghana da CFA na kasashe renon Faransa da ke kewaye da Najeriya, za a ga cewa darajar Naira ta fi kowannensu lalacewa.

Isa ya ce a yanzu haka CFA daya ta fi Naira daraja, saboda haka wannan rahoto da bankin duniya ya fitar haka ya ke tunda a yanzu ana canjin dala daya a matsayin Naira dubu daya.

Ya kuma ce Najeriya ta yi sake, saboda komai a kasar ya ta’allaka ne kan kudaden kasashen waje.

Jamilu Mohammed, ya ce a matsayinsa na dan Najeriya wannan rahoto abin takaici ne, domin in an duba za a lura cewa Najeriya tana da wasu ginshikai na tattalin arziki da zamantakewa wanda zasu iya shanye wannan barazanar da jijjiga da harkar canji ta kawo.

Jamilu ya ce wannan alama ce da ke nuna tattalin arzikin Najeriya ya samu koma baya a wannan dan tsakanin kamar yadda Bankin Duniya ya fitar, sai dai yana mai fatan kasa zata dawo da karfinta nan ba da jimawa ba.

Babban Bankin Duniya ya bada shawarar cewa bankunan kasar su ba da dama a yi hada-hadar Naira kan dala da sauran kudaden duniya.

Saurari Rahoton Medina Dauda Muryar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG