Bankin ya ce mai yiwuwa Ghana ba za ta iya cimma muradin ci gaba mai dorewa (SDG) kan rage radadin talauci ba, sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin duniya da aka yi a baya-bayan nan.
Da yake jawabi a wajen taron ranar kawar da talauci a Accra, Mista Pierre Laporte, darektan bankin duniya na yankin Ghana, Laberiya da Sierra Leone, ya ce hauhawar farashin kayayyaki da aka samu cikin shekaru biyu da suka gabata ya nakasa karfin sayen kayayyaki, yayin da kudaden shiga suka yi karanci.
Haka kuma tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu ne ya jefa wasu 'yan Ghana da dama cikin talauci.
Masanin harkokin kudi da tattalin arziki, Hamza Attijjany ya ce bayan wadannan dalilai ma, mafi karancin albashi da gwamnati ta gindaya wa ma’aikata ya kara sanya al’ummar Ghana cikin talauci.
"Idan mun waiwaya, gwamnatin Ghana ta ajiye kudade da bai kamata a biya ma’aikacin gwamnati kasa da haka ba; wato GHC 14. To, idan mutum zai yi aiki a biya shi GHC 14 a rana, wanda ba abinci kadai zai saya da shi ba, har da biyan wasu bukatu nan gaba. In dai haka ne, to yawan mutane (dake fama da talauci) ya dara na binciken Bankin Duniya."
Wasu ‘yan kasuwa a Ghana sun jaddada ikirarin na Bankin Duniyan, inda suka nuna cewa yanzu ba su samun kasuwa kamar yadda suka saba samu, kuma rashin kudi ne ke hana su zuwa sayen kaya.
A cewar Mista Pierre Laporte, samun aikin yi ga jama’a, ita ce hanya mafi inganci da za ta rage radadin talauci da rashin daidaito a kasar.
Don haka ya ce tilas ne masu tsara manufofi su kara himma wajen bunkasa tattalin arzikinsu, da kare marasa galihu, da zuba jari a inda zai samar da ingantattun ayukan yi, yadda za'a sami bunkasar amfani ga kowa.
Sai dai Hamza Attijjany ya kara da cewa, baya ga wadannan matakan da Mista Larpote ya zayyana, cimma muradin rage talauci ga Ghana zuwa shekarar 2030 zai yi wuya idan ba ta yi gyara a wasu bangarori ba.
"Yawan hauhawar farashin kaya, musamman kayan abinci; yawan faduwar darajar (kudin) Cedi; yakin Rasha da Yukren, domin dogaro da Ghana ke yi ga samun hatsi daga gare su. Sai dai shawara da za mu baiwa Ghana ita ce mayar da hankali kan harkar noma; ta waiwaya ta duba, a ina ne ake da matsala a harkar noma."
Alkaluma na nuna cewa, kusan mutane miliyan 700 a duniya suna rayuwa cikin matsanancin talauci, yayin da suke rayuwa a kan kasa da dalar Amurka 2.15 a kowace rana, kuma sama da rabi na rayuwa ne a yankin kudu da hamadar Sahara.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna