Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Rajistar Kananan Bindigogi Dake Hannun Fararen Hula

Gwamna Bazoum Mohamed da shugabanin kungiyoyin farar hula

Hukumomin Jamhuriyar Nijar da hadin guiwar kamfanin SONIMA sun kaddamar da ayyukan rajistar kananan bindigogin da ke hannun jama’a da nufin tantance fararen hular da suka mallaki makamai don takaita hadarin da ke tattare da rike bindiga ba akan ka’ida ba.

NIAMEY, NIGER - Kungiyar ECOWAS ce ta umurci kasashen Afrika ta yamma da su gudanar da irin wannan aiki da ke matakin magance matsalar yaduwar halatattun makamai a hannun ‘yan ta’adda da ‘yan takife.

Daruruwan mutanen da suka mallaki kananan makamai a Nijar sun yi rajistar bindigogin da ke rike a hannunsu a tsawon makwannin da aka yi na gudanar da wannan aiki da ake kira "Marquade des Armes" dake matsayin wani bangare na tunkarar kalubalen tsaron da ake fuskanta a kasar da ma yankin Afrika ta yamma baki daya.

Da yake karin bayani kan wannan shiri na kamfanin SONIMA Karimou Albert Paul ya nuna gamsuwa a kan yadda shirin ya samu karbuwa a wajen jama’a.

Daya daga cikin wadanda suka yi rajistar bingoginsu a wannan Talata 11 ga watan Afrilu wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya yaba da tsarin tafiyar da ayyukan rajistar.

Amintattun dillalan bindigogi ko kuma masu shagunan sayar da makamai da ake kira "Armurier" na taka rawa sosai a wannan shiri domin mataki ne da ka iya ba su kariya a matasyinsu na masu irin wannan sana’a.

Bayan birnin Yamai a nan gaba za a fadada wannan aiki zuwa jihohi domin kara kusantar fararen hular dake rike da makamai su sami damar yin rajistar kamar yadda kungiyar CEDEAO ta bukaci kasashe mambobinta su yi da zummar bambance halatattun makamai da na ‘yan bindiga a wannan yanki mai fama da matsalolin tsaro.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Nijar Sun Gudanar Da Rajistar Kananan Bindigogi Dake Hannun Fararen Hula.mp3