Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Ayyana Shirin Fara Rajistar Kananan Bindigogi Da Harsasan Da Farar Hula Suka Mallaka


Hoton bindigogi
Hoton bindigogi

Ma’aikatar cikin gidan Jamhuriyar Nijer ta bayyana shirin fara rajistar kananan makaman da ke hannun farar hula da nufin karfafa matakan zuba ido kan makaman da ke yawo a tsakanin jama’a.

Wannan wani mataki ne da ya biyo bayan yarjejeniyar da kasashen yankin ECOWAS suka cimma a ci gaba da neman hanyoyin tunkarar matsalolin tsaro.

A sanarwar da aka fitar a wannan makon ne ofishin Ministan cikin gidan Nijar ya bayyana shirin fara rajistar kananan makaman da ke hannun farar hula daga ranar 20 ga watan Janairun 2023, a saboda haka ya zama wajibi mutanen da suka malallaki bindigogi da harsasai su gabatar da su a ofishin kamfanin SONIMA domin su yi rajista, wato marquage kamar yadda kungiyar CEDAO ta umurci kasashe mambobinta.

Darakatan kula da sha’anin doka a ma’aikatar cikin gida Malan Zabei Alhaji Ibro, ya ce matakin yin rijistar na da muhimmanci sosai.

Ayyukan rajistar wadanda a watannin baya aka aiwatar da makamantansu ga wani rukuni na jami’an tsaro abu ne da a take aka ga fa’idarsa.

Shugaban jam’iyyar PNPD Akal Kasa Inticar Alhassan, wanda ke zaune a daya daga cikin yankunan da bindiga ke zama wani makamin kare kai daga aika-aikar barayi da ‘yan fashin dabbobi ya yi na’am da matakin na mahukunta, yana mai cewa rijistar zata ba da dama a san wadanda ke bindiga kuma wadanda basu yi rijistar ba za a dauke su a matsyain ‘yan ta’adda.

Kafin zuwan ranar soma ayyukan rajistar ma’aikatar cikin gida na ci gaba da fadakarwa game da muhimmancin samun hadin kan al’umma.

Jamhuriyar Nijar da ke makwaftaka da kasashen da ke fama da rikitar-rikita irinsu Libya, Mali, Burkina Faso, da wani bangare na Chadi, da Najeriya na matsayin wani wurin da masu safarar makamai ke yada zango akan hanyarsu ta shigar da bindigogi a wadannan kasashe.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

XS
SM
MD
LG