NIAMEY, NIGER - An dai gano kungiyoyin ta’adda suna amfani da yanayin talauci da jahilcin matasa don shigar da su ayyukan ta’addanci cikin salon yaudara.
Binciken da gidauniyar NEEM Foundation ta gudanar a yankunan dake fama da aika-aikar ‘yan bindiga a Najeriya, ya tabbatar da cewa kungiyoyin ta’addanci na amfani da salo irin na alkawuran karya, don kwadaitar da matasa shiga miyagun ayyukan da suke tafkawa, wanda sai bayan tafiya ta yi nisa su fahimci haka.
Mafarin da aka shirya wannan kamfe din kenan da aka yi wa lakani da “Lokacin Fadin Gaskiya”.
Haka makamancin wannan al’amari ke wakana a Nijar, a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro, dalili kenan kungiyoyi da cibiyoyin nazari da bincike akan batun zaman lafiya a kasashen biyu, suka hada guiwa domin fitar da jama’a daga duhu kamar yadda shugaban kungiyar COPAVE Harouna Saley Abdoulaye ya shaidawa sashen Hausa.
Kakakin kwamitin tsaro a Majalissar Dokokin kasa Lantana Oumarou na kallon wannan yunkuri da mahimmanci. Ta na mai bayyana fatan ganin an dauki matakai a hukunce don karfafa guiwar wadanan kungiyoyi.
Bukin kaddamar da wannan kamfe ya kasance wani lokaci na musanyar bayanai a tsakanin wakilan kungiyoyin da suka hallara tare da tsayar da wasu shawarwarin karshen taro.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma: