NIAMEY, NIGER - To sai dai kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawar sun bayyana fatan ganin an yi aiki da doka don ganin an hukunta masu laifi an kuma wanke wadanda ba su da hannu a ciki.
Binciken da hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA ta gudanar a ma’aikatar Douane ne ya bada damar bankado wata almundahanar da a ke zargin an tafka a zamanin da General na Jandarmomi Amadou Halidou da kanal Oumarou Amadou mai lakanin Petitot suka shugabanci hukumar ta DGD lamarin da ya sa aka kulle su a kurkuku a ci gaba da neman haske akan wannan cuwa cuwa da ta shafi million 16000 zuwa 18000 na cfa.
Jami’in fafutika ta yanar gizo Bana Ibrahim na daga cikin masu bin diddigin wannan labari.
Wasu majiyoyin hukumomi sun ayyana cewa dimbin jami’an Douane ne ake hasashen an hada baki da su wajen karkata akalar wadannan kudade saboda haka akwai yiyuwar wannan yunkuri ya rutsa da ma’aikata kusan 100.
Dalilin haka ne shugaban reshen kungiyar yaki da cin hanci Transparency International a Nijar, Malan Maman Wada ke gargadin mahukunta akan bukatar gudanar da lamura a karkashin abubuwan da doka ta yi tanadi ta yadda za a yi abin cikin yanayin adalci.
Shugabannin kungiyar jam’ian Douane ta SNAD da muka tuntuba sun sanar cewa suna gudanar da taron hadin gwiwa da shugabannin hukumar DGD da jami’an ma’aikatar ministan kudi saboda haka za su shaida mana bayan kammala wannan zama amma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba su wani bayani daga gurunsu ba.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5